1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta tura sojoji 650 a Mali

Zainab Mohammed AbubakarNovember 25, 2015

A yanzu haka dai Jamus tana da sojojinta 200 a banganren ayarin horar da jami'an Mali na Tarayyar Turai da ke yankin kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/1HCPR
Symbolbild Bundeswehr in Mali
Hoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Jamus za ta tura sojoji 650 zuwa kasar Mali da ke yankin yammacin Afirka, a wani mataki na taimakon Faransa a kokarinta na yaki da 'yan kungiyar IS. Ministar tsaro ta Jamus Ursula von der Leyen ta sanar da hakan, gabannin ziyarar shugabar gwamnati Angela Merkel a birinin Paris domin ganawa da Shugaba Francois Hollande na Faransa.

Ministar tsaron ta Jamus ta ce, za a gabatar wa majalisar dokoki wannan bukatar ta tura karin rundunar sojin 650 daura da 200 da ke can, wanda ke zama gudunmowar kasar a wannan yaki da ake yi da ayyukan tarzoma na IS.

A baya dai Jamus ta aike da sojoji 10 zuwa cikin tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke aikin kiyaye zaman lafiya, a yankin arewacin Malin da ke fama da rigingimu na 'yan tawaye, kuma tana shirin kara yawansu.