1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Zaman karshe na kulla kawance

February 6, 2018

Jam'iyyun siyasar Jamus za su yi zaman karshe don sama wa kasar makoma bayan zaben kasar da ya gaza bai wa jam'iyya mai mulki rinjayen da ya kamata ta sami ikon tafi da kasa yadda take bukata.

https://p.dw.com/p/2sAq6
Deutschland Bundestag Debatte zum Thema Antisemitismus | Übersicht
Zauren taron nema wa Jamus mafitaHoto: imago/C. Ditsch

A wannan Talatar ce ake sa ran Jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da SPD, za su kammala tattunawar kulla kawancen samar da gwamnatin hadaka, da ake ganin zata kawo karshen kiki-kakar siyasa da kasar da ta fi kowacce karfin arziki a nahiyar Turai ta shiga. Da misalin karfe goma na safiyar Talatar ne dai ake sa ran wakilan jam'iyya mai mulki ta CDU da CSU da kuma SPD za su yi ganawar da ake ganin ta karshe ce, bayan dogon turanci da aka sha jiya Litinin a kokarin da ake yi na cimma matsaya.

Manyan fannonin da aka sami tarnaki a zaman tattaunawar baya, su ne fannonin kudaden gudanar da harkokin kiwon lafiya da samar da ayyukan yi gami da na fannin tsaron kasa. Jami'an dai na bayyana fatar cimma kyakkyawar madafa a zaman da za a yi nan gaba a yau din.