1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jan Egeland da hukumomin Sudan

Zainab A MohammadApril 6, 2006
https://p.dw.com/p/Bu70

Wani babban jamiin mdd dake Khartum ya bayyana cewa,Sudan na fuskatar barazanar asarar tallafi wa miliyoyin alummanta dake bukatar agajin gaggawa,sakamakon hana jamiin agajin gaggawa na mdd,Jan Egeland ziyartar yankuna dake fama da wannan matsaloli.Coordinatan mdd dake Sudan Manuel Aranda da Silva yace idan har gwamnati na ganin cewa tana da ikon takaitawa kowa inda zaije,zasu iya amfani da kudaden tallafinsu wa wasu yankun da ake musu maraba.Yace makasudun zuwan Egeland Sudan,shine domin neman kudade da zaa tallafawa alummar kasar dashi,bayan ganin halin da suke ciki.Gwamnatin Khartum dai ta hana jamiin agajin gaggawan ziyartan Darfur ,da fadar gwamnatin kasar dake Khartum.Kazalika an hanashi bin sararin samaniyan lardin Darfur din ,akan hanyarsa ta zuwa sansanonin yan gudun hijira dake tchadi,wadda ke makwabtaka da Sudan din.Jan Egeland dai ya danganta wannan matsala da ya samu,da fita fili da yayi wajen bayyana irin halin da dakarun kungiyar Afrika dake kasar ke ciki,na neman tallafi.