1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridar Die Tageszeitung (TAZ) na bikin samun shekaru 25 da kafuwa

April 15, 2004

A ranar 17 ga watan afrilu na shekarar 1979 ne aka fara buga jaridar Die Tageszeitung (TAZ) ta masu zazzafan ra'ayin gurguzu a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/Bvkg
Dominic Johnson ya saba gabatar da sharhi da rahotanni akan al'amuran Afurka a Jaridar TAZ
Dominic Johnson ya saba gabatar da sharhi da rahotanni akan al'amuran Afurka a Jaridar TAZHoto: AP

Daya daga cikin dalilan da suka taka rawa wajen kirkiro jaridar da Die Tageszeitung, ta farko mai zazzafan ra’ayin gurguzu a yammacin Jamus, wacce aka fara bugata a daidai ranar 17 ga watan afrilun shekara ta 1979, shi ne dokar tace labarai da gwamnati ta kafa sakamakon garkuwa da kuma kisan shugaban gamayyar ‚yan kasuwar Jamus Hans-Martin Schleyer da aka yi a shekarar 1977. A lokacin da yake bayani game da haka Michael Sontheimer daya daga cikin masu alhakin kirkiro jaridar ta Die Tageszeitung cewa yayi:

Mutanen da suka yi hadin guiwa wajen kirkiro jaridar TAZ ba su da wata masaniya a game da aikin jaridanci. Babu daya daga cikinmu dake da wani ra’ayi a game da yadda ake tsara jarida. Dukkanmu dai ‚ya’yan kungiyoyin dalibai ne masu zazzafan ra’ayi na tsageranci, amma kuma mun gundura da yawon zanga-zanga a tituna, a saboda haka muka tsayar da shawarar bin wata manufa ta yada ra’ayinmu na juyin-juya-hali.

Bayan kai ruwa rana da aka sha famar yi sakamakon karancin kudi, musamman a shekarar 1984, jaridar ta farfado tana mai sabunta tsare-tsaren ayyukanta domin su dace da tafiyar zamani, ko da yake ma’aikatanta sun ci gaba da tsumulmular kudi ba sa facaka, irin wadda aka san ‚yan jarida da ita. Da yawa daga cikinsu su kan yi hadin guiwa wajen haya gidajen zama. To sai dai kuma sun sha fama da matsala a irin wannan zama na hadin guiwa musamman idan an samu sabani tsakaninsu, misali a wurin aiki, inda sabanin kan gurbata yanayin cude-ni-in-cude-ka a gidajen na hadin guiwa. A baya ga haka da yawa daga cikin ma’aikatan dake da ra’ayin tsageranci, ko da yake ba sa shan barasa, amma fa amfani da tabar wiwi ya zama ruwan dare tsakaninsu. Duk kuwa da wadannan fadi-tashi jaridar ta Die Tageszeitung ko kuma TAZ a takaice ta zama wata muhimmiyar cibiyar horar da ‚yan jarida mafi girma a duk fadin Jamus. Dukkan manyan jaridu da mujallun Jamus, kama daga Tagesspiegel da Frankfurter Allgemeine Zeitung da Zeit da Welt da Frankfurter Rundschau ko mujallar der Spiegel, dukkansu na da fitattun ‚yan jarida da suka samu kwarewarsu daga jaridar ta TAZ. A lokacin da yake bayani Thomas Hartmann babban editan jaridar na farko, wanda kuma ya dakatar da aikinsa a shekarar 1987 nuni yayi da cewar:

Tun abin da ya kama daga lokacin da aka kirkiro jaridar TAZ zuwa halin da muke ciki yanzun, ta zama tamkar wata kyakkyawar kafa ta samun ci gaba ga masu sha’awar aikin jaridanci. Kuma ba shakka zata ci gaba da kasancewa kan haka har kwanan gobe, lamarin da da wuya akan samu irin shigensa dangane da sauran jaridu da kafofin yada labarai.