1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Gano arzikin iskar Helium a Tanzaniya

Mohammad Nasiru AwalJuly 1, 2016

Rashin cin gajiyar arzikin karkashin kasa a Afirka, da rikicin siyasa a Madagaska da Zambiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/1JHXY
Tansania Präsident John Magufuli
Shugaba John Magufuli na Tanzaniya ya lashi takobin yaki da cin hanci da rashawaHoto: Getty Images/AFP/D. Hayduk

Za mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a wannan makon ta yi tsokaci game da gano arizin iskar Helium a kasar Tanzaniya.

Ta ce iskar ta Helium wadda ba ta da nauyi, kuma ake amfani da ita musamman a cikin balanbalan wata tawagar masu bunciken suka gano ta a yankin Rift Valley. Jaridar ta kara da cewa gano wannan arzikin karkashin kasar na zama wani albishir domin a shekarun baya wani masanin kimiyya ya yi hasashen cewa iskar ta Helium mai daraja a fannoni da dama, ta kusa karewa a duniya. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, inji jaridar tana mai cewa ko da yake gano Helium din babban albishir ne ga kasar Tanzaniya wadda karkashin sabon shugabanta John Magufuli ta daura dambar yaki da cin hanci da rashawa, amma idan aka dubi tarihin baya bayan nan za a ga cewa gano arzikin karkashin kasa na janyo wa kasashen Afirka karin matsaloli maimakon cin gajiyar wannan arziki.

Zaman dar-dar a Madagaska

Asarar rayuka bayan wani hari da aka kai a Madagaska inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.

Madagaskar Bombanschlag
Masu aikin ceto bayan harin bam da aka kai a MadagaskaHoto: Getty Images/AFP/Rijasolo

Ta ce akalla mutane biyu sun hallaka sannan fiye da 80 sun samu raunuka masu tsanani a wani harin gurnati da aka kai ranar Lahadi lokacin wani bikin kida a filin wasan kwallon kafa da ke Antananarivo babban birnin kasar Madagaska. Tuni dai shugaban kasa Hery Rajaonarimampianina ya ce harin ta'addanci ne inda ya zargi abokan adawarsa na siyasa da hannu a ciki. Tun a shearar 2009 Madagaska ta yi fama da rikicin siyasa da ya kusan jefa kasar cikin yakin basasa. Duk da cewa an samu kwarya-kwaryar kwanciyar hankali amma har yanzu ana fama da zaman dar-dar da rashin yarda da juna tsakanin jagororin siyasar kasar.

Rufe bakunan masu sukar gwamnati

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a wannan makon ta leka kasar Zambiya ne tana mai cewa yayin da ake dab da gudanar da zabe a kasar, gwamnati ce ke daukar matakan rufe bakunan masu sukar lamirinta.

Sambia Protest gegen Schließung von Zeitung in Lusaka
Zanga-zangar adawa da rufe gidan buga jaridar The Post a ZambiyaHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Mwape

Ta ce yanzu haka an rufe gidan buga jarida mai zaman kanta mafi girma a kasar da ke a babban birni wato Lusaka. Jaridar ta The Post ta gamu da fushin hukuma ne bayan an zargeta da rashin biyan kudin haraji da ya kai Euro miliyan 4.3. Sai dai a wani sharhi da ta rubuta a shafin intanet na jaridar, manejar gidan buga jaridar, Joan Chirwa ta bayyana matakin mahukuntan da wani yunkurin rufe gidan buga jaridar ta The Post gabanin zaben na watan Agusta. Kuma ba jaridar ce wata kafar yada labarai kadai da ta zargi gwamnati da kokarin yin magudin zabe ba, amma an yi amfani da zargin rashin biyan haraji a wani mataki na rufe bakunan masu sukar lamirin gwamnati.

Afuwa ga dan tsohon shugaban kasar Senegal

Godiya ta tabbata ga wata afuwa, Karim Wade dan tsohon shugaban kasar Senegal ya bar gidan yari tun hukuncin daurin da aka yanke masa bai kare ba inji jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce shugaban kasar Senegal Macky Sall ya yi wa Karim Wade afuwa daga daurin zaman gidan maza bayan kotu ta same shi da laifin yin sama da fadi da kudin kasa. Jim kadan bayan sakinsa daga kurkuku, Karin Wade ya tashi nan-take a cikin wani jirgin saman gwamnatin Katar zuwa Doha, kuma har yanzu yana zamansa a can.