1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Sabuwar nasara kan Boko Haram

Mohammad Nasiru Awal
December 30, 2016

Sake samun galaba kan Boko Haram a Najeriya da ci gaba a Ruwanda da siyasar kasar Somaliya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/2V3Tz
Nigeria Armee Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/H. Ikechukwu

Za mu fara sharhin jaridun na Jamus kana nahiyar ta Afirka da jaridar die Tageszeitung wadda a labarinta mai taken "Sake samun galaba kan Boko Haram" sannan sai ta ci gaba da cewa:

Kamar a shekarar 2015, a wannan karon ma Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bada sanarwar yin nasara kan masu tada kayar baya na kungiyar Boko Haram, yana mai cewa sojojin kasar sun kwace tungar kungiyar da ke a dajin Sambisa, sai dai tuni da yawa daga cikin mayakan na Boko Haram sun tsere zuwa wasu wuraren. Jaridar ta ce sanarwar na zama wani goron bikin Kirsimeti ga 'yan kasar. To sai dai kuma duk da ikirarin da sojojin kasar suka yi na kwace dajin Sambisan, har yanzu ba a ga sauran 'yan matan makarantar Chibok da wasu matan da ke hannun Boko Haram din ba. Abinda ke akwai shi ne tuni da yawa daga cikin mayakan na Boko Haram suka tsere zuwa yankin tafkin Chadi da yankin kan iyakar makociyar kasa Nijar.

Paul Kagame ka iya mayar da hannun agogo baya

Ruwanda za ta bata rawarta da tsalle, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai mayar da hankali kan kasar ta Ruwanda.

Shugaba Paul Kagame zai bata rawarsa da tsalle
Shugaba Paul Kagame zai bata rawarsa da tsalleHoto: World Economic Forum/Benedikt von Loebell

Ta ce kasar na zaman abin mamaki wajen aiwatar da canje-canje masu ma'ana a tsakanin kasashen Afirka. Inda abubuwa da dama suka inganta, tattalin arzikinta na bunkasa, yawan matalautanta na raguwa. Kimanin mutane miliyan daya dai suka rasa rayukansu a kisan kare dangin da ya auku a kasar a 1994, sannan kusan dukkan ginshakan tattalin arzikinta sun ruguje. Amma bayan shekaru 22 kasar ta farfado sai ka ce ba ta taba fuskantar wani bala'i ba. To sai dai a fannin shirya zabe na gaskiya da adalaci da bin tsarin demokradiyya, kasar na da nakasu. Yanzu haka ma shugaban kasa Paul Kagame na aiwatar da wani mulki shigen na kama-karya.

Jacob Zuma na raba kan jam'iyyar ANC

Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuya
Jacob Zuma na cikin tsaka mai wuyaHoto: Reuters/P. Bulawayo

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland a wannan mako ta leka kasar Afirka ta Kudu tana mai cewa Shugaba Zuma ya mayar da kanshi wani kadangaren bakin tulu.

Ta ce duk da badakalar da ta dabaibayeshi, shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma na ci gaba da rike madafun iko, lamarin da ke janyo wa jam'iyyar ANC bakin jini. Jaridar ta ce yanzu haka shugaban ya raba kan 'ya'yan jam'iyyar mai jan ragamar mulki. Ana dai zargin Shugaba Zuma da azurta kanshi da dukiyar kasa, kana ba ya shakkan cefanar da al'amuran kasar ga wasu manyan 'yan kasuwa.

Zabe mafi tsawo a duniya

A karshe za mu kuma sake duba jaridar die Tageszeitung amma a wannan lokaci ta yi tsokaci ne kan kasar Somaliya tana mai cewa:

Za a ci gaba da jiran lokacin gudanar da zabe mafi tsawo a duniya. Ta ce kasar ta Somaliya da bata da wata hukuma ko gwamnati tsayayya, tun a wasu watanni da suka wuce take ta shirye-shiryen zaben shugaban kasa amma aka yi ta dage lokacin. Ba al'ummar kasar ke zaben shugabansu ba, alhakin haka ya rataya kan wakilan majalisa su kimanin 275 daga jihohi shida na kasar. Tun a watan Oktoba aka fara wannan shirye-shirye sai dai ba a san lokacin da za a kammala shi ba.