1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Sabon rikici tsakanin Habasha da Eritriya

Mohammad Nasiru AwalJune 24, 2016

Rikicin kan iyaka a yankin Kahon Afirka da boren tsoffin 'yan tawayen Kwango da masu ci da gumin yara a Senegal.

https://p.dw.com/p/1JCBM
Äthiopien Soldat an der Grenze zu Eritrea
Tun shekaru gommai sojojin Habasha ke sintiri a kan iyakarta da EritriyaHoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Za mu fara da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda a wannan makon ta leka yankin Kahon Afirka tana mai mayar da hankali kan wani gumurzu na kan iyaka tsakanin kasashen Habasha da Eritriya.

Ta ce da haka yake-yake ke farawa, Eritriya da Habasha sun yi musayar wuta a kan iyakarsu, lamarin da ke yin tuni da munanan abubuwa. Jaridar ta ce sannun a hankali wani rikici ya kunno kai amma bai samu martani daga kasashen duniya ba saboda wasu rikice-rikice a yankin kamar ayyukan tarzoma a Somaliya da ya fi daukar hankalin duniya. Sai dai tasirin wannan rikicin ka iya kaiwa har nahiyar Turai, domin zai haddasa kwararar 'yan gudun hijira da ke tserewa daga rikicin da a 'yan kwanakin nan ya yi muni tsakanin kasashen biyu makwabtan juna. Tuni dai gwamnatin Eritriya ta mika kiran neman dauki daga Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da Habasha ke shirye-shiryen kaddamar da abinda ta kira gagarumin farmaki.

Tashin hankali a barikin sojin Kwango

Tsoffin 'yan tawaye na sha'awar komawa gida, inji jaridar Die Tageszeitung lokacin da ta garzaya Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango tana mai cewa tun shekaru hudu da suka wuce tsoffin mayakan 'yan tawaye ke jurewa da zama a wasu sansanoni, lamarin da ya janyo bore da tashin hankali.

Kongo Kämpfe in in Goma
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Kay

Jaridar ta ruwaito tsohon kwamandan 'yan tawaye Benjamin Matembera ya wallafa a shafin Facebook daga wani barikin soji da ke kudu maso yammacin Kwango cewa suna son su koma gida, kuma yana dokin sake ganin iyalinsa da ya kwashe tsawon shekaru hudu bai gansu ba. Shi dai Matembera daya ne daga cikin dubban mayakan kungiyoyin sa kai dabam-dabam a yankin mai fama da rikici da suka ajiye makamansu. Sai dai kwanaki kalilan bayan wannan furucin an yi harbe-harbe a barikin inda aka kashe tsoffin 'yan tawaye shida da sojoji uku. Musayar wutar ta auku ne lokacin wata zanga-zangar nuna takaicin yadda gwamnati ta kasa cika alkawarin da ta dauka na mayar da tsoffin 'yan tawayen gida.

Ci da gumin yara a Senegal

Bara da sunan Allah inji jaridar Neues Deutschland. Ta ce wasu makarantun allo a kasar Senegal na amfani da yaran da aka kaisu don a karantar da su Alkur'ani mai tsarki, a matsayin wata kafar samun kudaden shiga.

Die Bettel-Schüler aus Nordnigeria
Yawon bara: dadaddiyar al'adar tsakanin yaran makaratun alloHoto: DW

Jaridar ta ce dukkan yaran Musulmi a kasar Senegal suna zuwa makarantar karatun Alkur'ani, sai dai akwai bata gari a tsakanin makarantun, inda kuma ake ci da gumin kananan yaran, ana kuma ajiye su cikin wani mummunan yanayi da bai dace da rayuwar dan Adam ba. Akasari wadannan makarantun allon na bogi suna tura yaran yawon barace-barace a cikin gari, inda za ka ga yaran sun yi gungun gungu a kan titunan Dakar babban birnin kasar. Sai dai duk da haka akwai wasu kungiyoyin da ke aikin tallafa wa yaran da akasari daga kauyuka ne ake dauko su. Yanzu haka kuma ana wani kamfen na kawo karshen wannan al'ada.