1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Shekaru 40 da zanga-zangar dalibai a Soweto

Mohammad Nasiru AwalJune 17, 2016

Har yanzu da sauran aiki wajen daidaita al'amura a Afirka ta Kudu, shekaru 40 bayan zanga-zangar 'yan makaranta a Soweto.

https://p.dw.com/p/1J8yD
Südafrika 40 Jahre nach dem Schüleraufstand von Soweto
Hoto: picture-alliance/AP Photo/T. Hadebe

Jaridun na Jamus sun rubuta labarai masu yawa game da cika shekaru 40 da boren dalibai a Soweto. Alal misali jaridar Die Tageszeitung ta ce shekaru 40 da suka wuce 'yan makaranta suka fara bore a Soweto kuma zanga-zangar ta ranar 16 ga watan Yunin 1976 ta kasance mafarin abubuwan da suka kawo karshen gwamnatin mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu. Jaridar ta ce yara da matasa kimanin dubu 15 suka yi wani maci cikin lumana dauke da kwalaye suna tir da Afrikaans, harshen da gwamnati ta so ta yi amfani da shi a matsayin harshen koyarwa a makarantun kasar, lamarin kuma da ya janyo zanga-zangar. 'Yan sanda farar fata sun mayar da martani na rashin imani, sun bude wuta kan masu zanga-zanga inda suka hallaka daruruwan yaran makaranta.

A sanya wa wata makarantar sakandare a birnin Berlin sunan yaron nan dan shekaru 13 da ya kasance tamkar garzo a boren na 16 ga watan Yunin 1976 wato Hector Pieterson, wanda a cikin wani hoto aka dauko shi jina-jina bayan harbinsa a ka da 'yan sanda suka yi, inji jaridar Neues Deutschland. Ta ce ko da yake boren ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen mulkin wariyar launin fata, amma har yanzu mazauna Soweto musamman matasa na fama da matsalar rashin aikin yi kana akwai makeken gibi a fannin ilimi tsakanin al'ummomin kasar.

Sabon rikicin kan iyaka tsakanin makwabta

Marikita a yankin Kahon Afirka inji jaridar Neue Zürcher Zeitung tana mai mayar da hankali kan wani gumurzu tsakanin kasar Habasha da Eritriya da ke zama tsoffin abokan gaba.

Äthiopien Soldaten
Sojoji musamman na Habasha suna sintiriHoto: picture-alliance/dpa/S. Morrison

Ta ce a cikin kwanakin da suka wuce rigingimu sun girgiza yankin kan iyaka tsakanin Eritriya da Habasha, abin da ya sa Habasha da ke zama babbar kasa ta yi barazanar kaddamar da abinda ta kira gagarumin yaki a kan karamar makwabciyarta ta. Eritriya dai ta zargi Habasha da kai hari kan iyakarta, zargin kuma da gwamnati a birnin Addis Ababa ta gaskata, amma ta ce mataki ne da ta saba dauka a kan tsokanar da Eritriya ke mata. An dai samu asarar rayuka daga bangarorin biyu. Jaridar ta Neue Zürcher Zeitung ta ce zai yi wahala a gane kasar da ta fara kai harin, amma ta ruwaito 'yan adawa a Eritriya na cewa gwamnati a birnin Asmara za ta yi maraba da rikicin don cigaba da tursasa wa matasa su shiga aikin soji.

Toshe hanyoyin sadarwa ta intanet

Symbolfoto Terrorismus und Social media
Shafukan sada zumunta na intanet na taka rawa a fagen siyasaHoto: picture-alliance/AP Photo/E. Vucci

Matakan dakile tura sakonni ta shafukan sada zumunta inji jaridar Neues Deutchland tana mai cewa gwamnatocin Afirka da dama na kokarin takaita hanyoyin sadarwa na intanet don rufe bakunan masu sukar lamirinsu. Jaridar ta ce a kullum wasu kasashen Afirka na toshe hanyoyin intanet a lokacin da kasa ke shirye-shiryen gudanar da zabe. Ga misali kasar Ghana na shirin toshe shafukan sada zumunta na intanet a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da za a gudanar a cikin watan Nuwamba mai zuwa. Wasu kasashe irinsu Yuganda da Kwango-Brazaville sun taba daukar irin wannan mataki. Shakka babu shafukan sada zumunta na intanet na taka muhimmiyar rawar fadakarwa musamman a fagen siyasa a Afirka.