1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun duba shekaru uku na 'yan matan Chibok

Abdullahi Tanko Bala
April 14, 2017

Skaru uku tun bayan da 'yan Boko Haram da ke ikrarin musulunci suka sace daruruwan yara 'yan mata 'yan makaranta, sojoji suka kaddamar da farmaki domin kakkabe su a kowane loko da sako.

https://p.dw.com/p/2bFcI
Nigeria Abuja Reaktion angehörige nach Video über Chibok Girls
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Jaridar ta ce a yanzu sojojin na da cikakken iko da tsaro a kusan dukkanin yankunan kama daga Benisheikh a Maiduguri, zuwa ga sauran yankuna na yankin Arewa maso Gabas. Jaridar ta die Tageszeitung ta yi nuni da cewa a watan Satumba na shekarar 2013 aka yi mummunan gumurzu lokacin da 'yan Boko Haram suka yi kokarin danganawa da Maiduguri domin mayar da birnin karkashin ikon su. jama'a da dama sun gudu yayin da akan hanya fasinjoji matafiya su kimanin 170 da ke cikin motoci 'yan Boko haram suka yi musu yankan rago. Gwamna Kashim Shattima ya yi alkawarin sake gina gidajen da aka kona.

Kokarin sojojin Najeriya wajen yaki da Boko Haram

Nigeria Soldaten in Damboa
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Jaridar ta ce a yau garin Benisheikh ya kasance alamar kwarin zuciya da kyakyawar fata ta makoma mai kyau tare da burin cewa lokaci ne kawai ya rage Boko Haram ya zama tarihi. Mutane kimanin dubu 33 da suka tagayyara wadanda kuma aka tsugunar da su. sai daga cikin wannan adadi dubu 20 suka sami shiga cikin jadawalin da aka tantance na tsarin samun tallafi.

Jaridar ta die Tageszeitung ta ce a lokacin da ake tsakiyar yaki da Boko Haram gundumomi 24 daga cikin gundumomi 27 suna hannun Boko Haram, inda suka yi garkuwa da mazauana yankunan tare da lalata musu dukiya da kadarori. Jaridar ta ce a yanzu al'amura sun sauya, yankuna biyu ne kacal ke hannun yan kungiyar ta Boko Haram. Sai dai kuma a cewar jaridar har yanzu akwai babban kalubale da ake fuskanta na wadata mutanen da ke zaune a sansanoni da abinci.

Tallafin Faransa da Jamus a yankin Sahel

Deutschland Bonn Ursula von der Leyen
Hoto: picture-alliance/dpa/I. Fassbender

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a sharhinta mai taken tallafin Paris da Berlin akan Sahel, ta ce kasashen Jamus da faransa sun jaddada kudirinsu na karfafa taimakon hadin gwiwa ta fuskar soji ga nahiyar Afirka wanda ministocin tsaro na kasashen biyu suka amince da shi.

Jaridar ta ce manufar taimakon na tsaro da na horon soji ga Afirka shi ne domin karfafa nahiyar ta Afirka kudu da Sahara wadda ke cikin kungiyar kasashe biyar na kungiyar G5 Sahel da suka hada da Mali da Mauritaniya da Niger da Burkina Faso da kuma Chadi. Bugu da kari a cewar jaridar ta Frankfurter Allgemeine Zeitung kawancen zai bada tallafi ga yaki da ta'addanci a yankin, inda tuni kasashen biyu na Faransa da Jamus suke da sansani a Yamai.