1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun yaba da zaben Najeriya

Mohammad Nasiru AwalApril 3, 2015

A sharhunan da suka rubuta game da nahiyar Afirka a wannan makon, jaridun na Jamus gaba ki dayansu sun mayar da hankali ne kan Najeriya.

https://p.dw.com/p/1F2TM
Nigeria Wahlen Wahlbeobachter
Hoto: DW/Scholz/Kriesch

Jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta fara sharhinta da cewa Najeriya ta yi waje road da cin hanci da rashawa. Jaridar ta ce babban sakon da ya fito daga kasar ta fi kowace yawan al'umma a nahiyar Afirka shi ne a karon farko cikin tarihinta dan adawa ya ka da shugaba mai ci ta hanyar zabe na demokaradiyya. Jaridar ta ce mafi rinjayen 'yan Najeriya sun zabi Janar Muhammadu Buhari domin sun yarda da alkawarin da ya dauka na kawo canji mai ma'ana a kasar, musamman wajen magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi kwai ta kyankyashe a cikin kasar, da kuma rashin kishin kasa. Jaridar ta ce sauyin da aka fara gani a bayan bore al'umma a Senegal da Burkina Faso yanzu an gani a Najeriya amma cikin ruwan sanyi da lumana.

Mai hakuri shi kan dafa dutse ya sha romo

Nigeria - nominierter Präsidentschaftskandidat Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya mai jiran gado Muhammadu BuhariHoto: Getty Images/P. Ekpei

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi amfani da wannan karin magana, inda ta ce nasara bayan yunkuri sau hudu. Ta ce ganin sai a wannan karo Muhammadu Buhari ya samu nasara a zaben shugaban kasar Najeriya, to godiya ta tabbata da kawancen manyan jam'iyyun adawa da suka kafa jam'iyyar APC.

Ta ce jam'iyyar ta rikide daga matsayin jam'iyya ta wani yanki zuwa babbar kungiyar al'umma Najeriya baki daya, wadanda suka yi alwashin kawar da jam'iyyar PDP daga kan karagar mulki ta yim wa babakere tun bayan komawar kasar bin tsarin demokaradiyya a shekarar 1999, jam'iyyar kuma da ta yi kaurin suna wajen cin hanci da gazawa.

Yaki da cin hanci da ta'addanci

'Yan Najeriya sun samu kwarin guiwa sai dai a matakin farko dole Buhari da ya yi nasara a zaben ya ba da fifiko wajen yaki cin hanci da rashawa da kuma ayyukan ta'addanci na Boko Haram, inji jaridar Berliner Zeitung.

Nigeria Erfolge der Offensive im Kampf gegen Boko Haram
Yaki da tarzoma na daga cikin manyan kalubalen da ke gaban sabuwar gwamnatiHoto: Reuters/Emmanuel Braun

Jaridar ta ce ba safai ake samun wani labari mai fararta rai musamman a fannin siyasar nahiyar Afirka ba. Amma idan ta faru, to tana da muhimmanci kwarai da gaske. Ta ce a cikin kwanakin nan Najeriya na cikin wani yanayi shigen na lokacin Nelson Mandela a Afirka ta Kudu bayan kawo karshen mulki nuna wariyar launin fata. Fata dai shi ne kwalliya ta biya kudin sabulu. Ko shakka babu aikin da ke gaban gwamnatin da za ta ja ragamar mulkin kasar nan gaba na da yawa sosai. Amma idan ta jajirce kuma ta samu hadin kan 'yan kasa to za ta kai gaci.

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta bi sahun jaridun na Jamus wajen tofa albarkacin bakinta game da sakamakon zaben na Najeriya, inda ta ce a karshe Goodluck Jonathan ya dauki waya ko da yake ba abu ne mai sauki ba, ya kira abokin hamaiyarsa Muhammadu Buhari, kana ya taya shi murnar lashe zaben. Wannan matakin da shugaban mai barin gado ya dauka ya zama wani muhimmin abin alfahari kuma abin a yaba da ya yi a tsawon wa'adin mulkinsa.