1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus: Tashin hankali a Sudan ta Kudu

Mohammad Nasiru AwalJuly 15, 2016

Mummunan fadan da ya barke a birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu ya fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/1JPfQ
Südsudan Juba SPLA Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/S. Bol

A labarin da ta buga game da rikicin jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa yaki ya dawo, shekara guda bayan yarjejeniyar zaman lafiya an sake gwabza fada da ya yi sanadin rayukan akalla mutane 300 a Sudan ta Kudu. Tambayar da 'yan kasar ke yi ita ce shin wa ya tada sabon fadan da ke barazanar jefa kasar cikin sabon yakin basasa? A watan Afrilu Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar sun kafa gwamnatin rikon kwarya biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiyar ta bara. Ko da yake mutanen biyu sun dade ba sa ga maciji da juna, amma bisa ga dukkan alamu an samu mutum na uku dangane da sabon rikicin, wato Paul Malong hafsan sojojin Sudan ta Kudu kuma mai tsauttsauran ra'ayin dan kabilar Dinka da ke kokarin ganin kabilarsa ta mamaye al'amuran kasar, ana yi masa kallon wanda ke da karfin fada a ji a gwamnatin Shugaba Kiir.

An kai Turawa tudun mun tsira

A game da rikicin na Sudan ta Kudu jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr ta kwashe Turawa daga Sudan ta Kudu zuwa tudun mun tsira. Ta ce yayin da shirin tsagaita wuta ke aiki a Juba wani jirgin saman yakin Jamus ya kwashe wasu Jamusawa musamman ma'aikatan ofishin jakadancin kasar da na wasu kungiyoyin agaji da ma wasu 'yan kasashen Turai daga Sudan ta Kudu zuwa Kampala babban birnin kasar Yuganda. Sai dai wasu Jamusawa da ke aikin sa ido karkashin Majalisar Dinkin Duniya za su cigaba da zama a kasar.

Amincewa da kisan kiyashi bayan shekaru 110

Namibia Friedhof der Herero- und Nana Stämme
Makabartar shugabannin kabilun Herero da Nama a NamibiyaHoto: picture-alliance/dpa/R. Kaufhold

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung a wannan makon sharhi ta rubuta game da amincewar da Jamus ta yi cewa lalle sojojin kasar sun aikata kisan kiyashi kan al'ummomin Herero da Nama na kasar Namibiya a yakin da aka yi a yankin da a lokacin ake kira yankin mulkin mallakan Jamus na Kudu maso Yammacin Afirka daga shekarar 1904 zuwa 1908 da yayi sanadin rayukan 'yan Afirka kimanin dubu 95. Jarida ta ce ko da yake an yi latti wajen amincewa da aikata kisan kiyashin a kan wadannan al'ummomi da suka tada boren kin mulkin mallakan na Jamus, amma amincewar na kan kyakkyawar turba kuma bajinta ne da ya zo shekaru 110 bayan aikata wannan ta'asa. Jamus dai ta yi wa Namibiya mulkin mallaka a lokacin da ake kiranta da suna Kudu maso Yammacin Afirka a tsakanin shekarar 1884 zuwa 1915.

Bunkasa ilimin yara a Senegal

Kenia Schulklasse in Nairobi
Samar da azuzuwa don bunkasa ilimin yara a SenegalHoto: picture-alliance/Photoshot

A karshe sai jaridar Kölner Stadt-Anzeiger wadda ta yi tsokaci kan wani aikin gina makaranta a wani kauyen da ek kasar Saliyo da wasu dalibai na birnin Kwalon a nan Jamus ke daukar nauyinsa.

Ta ce daliban birnin Kwalon sun shiga cikin kungiyar agaji ta L'appel don tallafa wa yara a Saliyo, kuma yanzu haka daliban da ke karatun koyon aikin likita suntara kudi Euro dubu 150 da za su aikin gina makarantar mai azuzuwa bakwai don bada darasi ga yara a lardin Bombali na kasar Saliyo. Daliban su kimanin 30 da ke karkashin kungiyar agajin ta L'appel suna kuma ba da agaji ga wani asibitin kasar Ruwanda.