1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jihar Taraba ta faɗa cikin ruɗani

Usman ShehuAugust 28, 2013

Rikicin siyasa ya rinchabe a jihar Taraba, inda yanzu aka rasa wake da hakikanin iko da gwamnatin Jihar.

https://p.dw.com/p/19Y3D
Treffen nigerianischer Gouverneure. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja
Majalisar gwamnonin NajeriyaHoto: DW

Gwamnatin jihar Taraba ta sanar da rusa majalisar zartarwar jihar. Yayin da yake bada sanarwa a yau Laraba a garin Jalingo, mai baiwa gwamna Danbaba Suntai shawara kan harkokin watsa labarai Mr. Sylvanus Giwa ya ce rusa majalisar zartarwar ya shafi kwamishinoni da kuma mashawartan gwamna na musamman. Wakilinmu Muntaqa Ahiwa wanda yake birnin Jalingo, yace ka zalika Mr. Sylvanus Giwa ya sanar da nadin Mr. Gideon Kataps a matsayin sabon Sakataren gwamnatin jihar da kuma Malam Aminu Jika a matsayin shugaban m'aikatan fadar gwamnatin jihar ta Taraba. Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa nadin nasu ya fara aiki nan take.

Wannan mataki dai ya kawo ruɗu a jihar ta Taraba, inda a dai-dai lokacin da majalisar dokokin jihar ke tabbatar da ce wa har yanzu, muƙaddashin Gwamnan Jihar Alha Garba Umar shine gwamna mai riƙo a Jihar Taraba, kuma a sanin majalisar kamar yadda kakakinta ya bayyana, ba su kai ga amincewar lafiyar gwamna Suntai ba, balle su ce an mayar masa muƙaminsa. Inda majalisar ta gayyaci gwamnan jihar dake fama da larurar rashin koshin lafiya, ya bayyana gaban ta domin tabbatar da kuzarin iya jagorancin jihar, bayan dawo da shi da aka yi ranar Lahadin da ta gabata, inda har izuwa yanzu, babu wanda yace ya yi magana da shi, kuma ba ji sautinsa ba a ko wace irin kafar yada labarai.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu