1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin Indunesiya ya faɗi da fasinjoji

Yusuf BalaAugust 16, 2015

Jirgin na Trigana Air na tafiya ne a samaniya daga garin Jayapura zuwa birnin Oksibi na Papua nan fa aka dena jin ɗuriyarsa daga filin tashi da saukar jiragen sama na Oksibi.

https://p.dw.com/p/1GGOn
Flugzeug Trigana
Jirgin Trigana AirHoto: picture-alliance/dpa/B. Indahono

Wani jirgin fasinja ɗauke da mutane 54 ya ɓace a ranar Lahadin nan a lokacin da yake kan hanyar yin wata taƙaitacciyar tafiya a Indunesiya, wasu rahotanni sun ce jirgin ya faɗi ne a yakin tsaunika a lardin Papua saboda matsalar yanayi da ake fiskanta mara kyau a ƙasar Indunesiyar, mazauna wani ƙauye a gabashin na Papua sun bayyana cewar sun ga lokacin da jirgin sama ya faɗi a yankin da ke da tsaunika.

Jirgin na Trigana Air na tafiya ne a samaniya daga garin Jayapura zuwa birnin Oksibi kusa da Papua New Guinea nan fa aka dena jin ɗuriyarsa daga filin tashi da saukar jiragen sama na Oksibi kamar yadda Julius Barata mai magana da yawun ma'aikatar sufuri a ƙasar ya bayyana.

Jirgin mai lamba ATR42-300 na ɗauke da fasinja 49 da masu aiki cikin jirgin biyar na kan hanya a wata tafiya da zai kwashe mintina 42. Wasu kafafan yaɗa labarai na ƙasar ta Indunesiya sun bayyana cewar ilahirin fasinjojin 'yan ƙasar ne ta Indunesiya, sai dai kamfanin jirgin saman bai bayyana waɗanda ke cikinsa ba.