1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta kai shawagi kusaa da tsibirin China

Yusuf BalaOctober 27, 2015

Wannan tsibiri da ake ganin China na ginawa dan jibge makaman yakinta, ana ganin kuma ka iya zama barazana ga harkokin sufuri dan kasuwanci tsakanin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/1Gugn
USA Zerstörer USS Lassen
Jirgin ruwan sojan AmirkaHoto: Reuters/U.S. Navy/Mass Communication Specialist 1st Class Martin Wright

Wani jirgin ruwan yaki mallakar kasar Amirka ya kai shawagi kusa da tsibirin da mahukuntan birnin Beijing suka gina a tekun Kudancin China kamar yadda jami'ai a ma'aikatar tsaron kasar ta Amirka suka bayyana, wani lamari kuma da ake wa kallon zai iya harzuka mahukuntan na China.

Wannan yanki dai da jirgin kasar ta Amirka ya kai shawagi na zama wuri da ake takaddama akansa da makwabtan kasar ta China abin da kasar ta China ta ce ya sabawa yarjejeniyar ratsa ruwan kasa da kasa, sai dai Amirkar ta ce yankin baya cikin waccar yarjejeniya kasancewar gina tsibirin China ta yi da kanta.

Kasashe da dama da ke makwabtaka da China ciki kuwa harda Philipines da ke zama kawa ga Amirka na adawa da China kan ikirarin mallakar wannan tsibiri da ake ganin China na ginawa dan jibge makaman yakinta, wanda kuma ka iya zama barazana ga harkokin sufuri dan kasuwanci tsakanin kasa da kasa.