1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jirgin yakin Taiwan ya yi batan dabo

Gazali Abdou Tasawa
November 8, 2017

Rundunar sojojin sama ta kasar Taiwan ta sanar a wannan Laraba da dakatar da tashin jiragen yakinta samfurin Mirage bayan da daya daga cikin jiragen yakin nata da matukinsa suka yi batan dabo lokacin wani atisaye.

https://p.dw.com/p/2nF75
Syrien Frankreich Luftschläge
Hoto: picture-alliance/dpa/Amboise /Ecpad/Sirpa Air Hand

Rundunar sojin kasar ta Taiwan ta ce da misalin karfe 10 da mintoci 43 agogon GMT ne wato mintoci 34 bayan tashin jirgin yakin na Mirage 2000 da matukinsa Ho Tzu-yu na'urar hangen jirgi ta daina ganinsa. Mahukuntan kasar ta Taiwan sun sanar da tanadin wasu jiragen sama 17 da na ruwa 10 na yaki domin cigiyar jirgin. A shekara ta 1992 ne dai kasar Taiwan ta yi odar jiragen yakin samfarin Mirage kirar Faransa guda 60. A shekara ta 2012 ma dai kasar ta taiwan ta dakatar da aiki da jiragen na Mirage a cikin wani gajeran wa'adi bayan da daya daga cikinsu ya rikito a kasar faransa tare da halaka matukinsa.