1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juncker: Turai na bukatar hada kai

Mohammad Nasiru Awal YB
September 12, 2018

A wani jawabi da ya yi a Majalisar Turai da ke birnin Strassburg, Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker, ya ce dole ne nahiyar Turai ta dage ta zama tsintsiya madaurinki daya don zama babbar daular duniya.

https://p.dw.com/p/34kz0
Europäisches Parlament in Straßburg | Rede zur Lage der EU von Jean-Claude Juncker
Hoto: Reuters/V. Kessler

A cikin jawabin na Jean-Claude Juncker ya tabo batutuwa da dama ciki har da dangantaka da Amirka da Birtaniya bayan ta fice daga Kungiyar EU, sai kuma batun zuba jari a nahiyar Afirka.

A jawabinsa na shekara kan halin da Kungiyar Tarayyar Turai ta EU ke ciki, shugaban hukumar kungiyar ta EU, Jean-Claude Juncker da ke cikin shekararsa ta karshe a matsayin shugaban hukumar, ya yi kira ga kasashen EU da su shawo kan bambamce-bambamcen da ke tsakaninsu a kan kasafin kudi da batun bakin haure da sauran batutuwa domin su samu sukunin cafke wata dama ta zama ja-gaba a harkokin siyasar duniya, yana mai cewa idan Turai ta yi magana da murya guda za ta iya karfafa matsayinta kan sauran kasashe.

Europäisches Parlament in Straßburg | Rede zur Lage der EU von Jean-Claude Juncker
Jean-Claude Juncker bayan kammala jawabi a StrassburgHoto: Reuters/V. Kessler

Juncker ya ce idan ana son a cimma wannan buri dole ne a kawo karshen abin da ya kira wasan kwaikwayo na raba kan kasashen Turai a gabas da yamma da kuma kudu da arewa. Ko da yake bai ambaci sunan wata kasa ba, amma ana ganin wannan furucin shagube ne ya yi ga kasashen Poland da Hangari.

Da ya koma kan batun bakin haure da dangantaka da Afirka kuwa Juncker cewa ya yi ya kamata EU ta gabatar wa Afirka yarjejeniyar ciniki maras shinge da kulla sabon kawance na zuba jari a wani mataki na samar da kyakkyawar makoma da habaka tattalin arzikin nahiyar Afirka da ke zama makwabciya mafi kusa da nahiyar Turai, wadda kuma matasanta ke bi ta hanyoyi masu hadari don yin kaura zuwa Turai.

Europäisches Parlament in Straßburg | Rede zur Lage der EU von Jean-Claude Juncker
Zaman Majalisar Tarayyar TuraiHoto: Reuters/V. Kessler

Kan batun Birtaniya kuwa, Juncker ya ce Tarayyar Turai za ta ci gaba da inganta huldar kasuwanci da tsaro da Birtaniya bayan ta fice daga Tarayyar Turai a badi idan Allah Ya kaimu.