1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyayi game da mutuwar Mandela a duniya baki daya

December 6, 2013

Jaridun Jamus kamar dai takwarorinsu na sauran duniya, sun maida hankali ga rasuwar gwarzon Afirka ta Kudu Nelson Mandela

https://p.dw.com/p/1AUH5
Hoto: picture-alliance/dpa

A yayin da duniya gaba daya take juyayi da zaman makoki saboda mutuwar tsohon shugaban Afirka Ta Kudu, kuma gwarzon gwagwarmayar neman yancin bakar fatan kasar, Nelson Mandela ranar Alhamis da dare, su ma jaridu a nan Jamus sun cika da rahotanni ne na yabon gwarzon a zamanin rayuwarsa.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tace Mandela tun a zamanin rayuwarsa ya zama gwarzo da duniya gaba daya tayi alfahari dashi. A gwagwarmayar da yayi na tabbatar da yanci da daidaituwa da kuma sulhu tsakanin juna, ana iya kwatanta shi da Mahatma Gandhi. Afrika Ta Kudu babu shakka tayi asarar danta mafi daukaka a duniya. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ambaci shugaban Afirka ta kudu mai ci, Jacob Zuma yana cewa Neson Mandela ya hade mu wuri guda, saboda hada gaba daya a hadenmu zamu yi sallama da Madiba, sunan Mandela na gargajiya. Mandela ya rasu ne ranar Alhamis sakamakon ciwon huhu da ya dauko tun yana tsare a gidan kurkuku a tsibirin Robben, inda yayi shekaru 27 yana tsare saboda gwagwarmayar yaki da mulkin wariya. Mandela an sake shi daga gidan kaso ne a farkon shekara ta 1990, inda aka zabe shi a matsayin shugaban kasa bakar fata na farko a Afirka ta kudu a yantaccen zabe na farko a shekara ta 1994. Shekara guda kafin hakan, Mandela, tare da shugaban karshe na zamanin mulkin wariya, Frederic de Klerk suka samki lambar Nobel ta zaman lafiya.

Jaridar Tageszeitung ita ma ta maida hankalinta ne kan mutuwar Mandela. Tace duniya gaba daya tana zaman makoki bayan rasuwar Nelson Mandela, mutumin da ya zama alamar yanci da sulhu ba ma a kasarsa Afirka ta Kudu kadai ba amma har a nahiyar Afirka baki daya. Tace ba'a taba samun wani lokaci da duniya baki daya ta hada kai a juyayin rasa ani gwarzo kamar ydada ake ciki yanzu bayan mutuwar Nelson Mandela ba. Yanzu, inji jaridar Tageszeitung tilas ne Afrika ta kudu ta koyi rayuwa ba tare da gwarzonta, Nelson Mandela ba.

Juyayin mutuwar Nelson Mandela
Hoto: Reuters/Mike Theiler

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung tayi sharhi mai tsawo kan Nelson Mandela inda tace dan gwagwarmaya da mulkin wariya, a zamanin rayuwarsa, ya baiwa Afirka Ta Kudu wata sabuwar fuska da sabuwar alkibla da kyakkyawar makoma. Jaridar ta yabi Mandela a matsayin mutumin da har ya mutu bai yi watsi da akidrsa ta neman sulhu da zaman lafiya tsakanin dukkanin Afirka ta kudu. Dangane da haka, mandla ya zama abin tunawa da za a dade ana juyayin rashinsa a nahiyar Afirka da duniya baki daya.

Rashin gwarzon na Afrika ta kudu shine dai abin da ya dauki hankalin jaridar Neue Zürcher Zeitung, wadda tace rayuwar sadaukar da kai da Nelson Mandela yayi, tattare take da tarihin rayuwar Afirka ta kudu baki daya. Bayan haka nan ma, jarumin zai ci gaba da zama abin koyi da misai ga duniya baki daya a fannonin shugabanci da sulhu da neman zaman lafiya. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace akwai shugabannin dake da zarfin zuciya, dake tsayawa tsayin daka a fagen mulki na-gari. Akwai shugabannin da tarihin ba zai taba mantawa dasu ba akwai kuma shugabanni dake zama jagoran siyasa. Mandela ya hade duka wadannan al'amura gaba daya, kafin ya rasu bayan rayuwar shekaru 95 a duniya.

A wani labarin kuma, jaridar Süddeutsche Zeitung ta tabo taron koli tsakanin kasashen Afirka da Faransa a Paris. Tace ko da shike tsohuwar uwargijiyar ta kasashen Afirka da dama bata kaunar ci gaba da shisshigi da sojojinta a wannan nahiya amma tashin hankali a Mali da Jamhuriyar Afika Ta Tsakiya sun hana ta cika wannan buri. Saboda haka ne daga cikin al'amuran da taron kolin ya duba a bana, har da yadda za'a shigar da kasashen Afirka sosai a yunkurin shawo kan matsalolinsu da kansu da kuma irin gudummuwar da Faransa za ta bayarwa dangane da haka.

Bildergalerie Leben Nelson Mandela
Mandela da shugaban karshe na zamanin wariya, F.W. d Klrk dauke da lambar NobelHoto: picture-alliance/AP

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Mouhamadou Awal