1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kada kuri'a cikin matakan tsaro a Iraqi

April 30, 2014

Al'ummar Iraqi sun fito domin kada kuri'unsu a babban zaben kasar na 'yan majalisu duk kuwa da firgicin da ake ciki na barazanar tashin bama-bamai a kasar.

https://p.dw.com/p/1BrlI
Hoto: Reuters

Rahotanni sun bayyana cewa al'ummar Iraqin sun kada kuri'unsu cikin tsauraran matakan tsaro na kota kwana da jami'an tsaron kasar suka dauka. Sai dai matakan da suka dauka din ba su hana kai wasu jerin hare-hare a yammacin Bagadaza babban birnin kasar ba wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan akalla mutane biyar tare kuma da raunata wasu 16. Wanna dai shi ne karo na farko da ake gudanar da zabe a Iraqin tun bayan da dakarun Amirka suka fice a kasar a shekara ta 2011. Dubun-dubatar mutane ne dai suka hallaka a ci gaba da fadan banbancin akida da kasar ke fama da shi yayin da wasu kuma da dama suka kauracewa gidajensu. Da dama dai daga cikin mutanen dake zaune a unguwannin Musulmi mabiya Sunna sun kaurace wa rumfunan zaben.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal