1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bobs-Voting startet

April 2, 2014

Takura wa marubuta, tonon sililin da Snowden ya yi, kan satar bayanan kasashe da Amirka ke yi, da rikicin Ukraine, su ne batutuwa da marubutan Blogs suka mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/1Ba7S
Deutsche Welle The Bobs 2014
Hoto: DW

A wannan Larabar ce aka fara kada kuri'a domin zaben fitattun marubutan fafutuka a shafin yanar gizo da aka fi sani da suna Bobs. Inda a kan yi nazarin ayyukan marubutan na Blogs a fafutukarsu na nemar wa al'umma 'yanci.

Marubuta a shafin yanar gizo na kasa da kasa, sun samu muhimman batutuwa na tsokaci a kai a wannan shekarar. Har yanzu dai 'yan jarida da masu shafin Blogs na ci gaba da fuskantar takura a duniya baki daya. Batun tatsar bayanai a asirce da hukumar leken asirin Amurka ta NSA, ya janyo kirkirar wasu sabbin dabaru, wanda ya jagoranci kirkirar sabbin fasahun zamani da ake amfani da su wajen sadarwa. Har yanzu ba a manta da zanga-zangar da suka gudana a kasar Turkiyya a lokacin bazarar shekara da ta gabata ba. Kazalika muhimmin batu da ya fi daukar hankali a farkon wannan shekara shi ne, rikicin siyasar kasar Ukraine. A nahiyar Afirka da Asiya kuwa ci gaba aka samu na ingantuwar fasaha, wanda ya ba wa al'umma damar samun bayanai a saukake.

Wani abun la'akari dangane da lambar yabo ta Bobs shi ne, yawancin marubutan Blogs da masu shafukan yanar gizo da marubutan fafutukar neman 'yanci da kare hakkin dan Adam, mutane ne da suka fuskanci takura da ma barazanar jefa su kurkuku a kasashensu na asali. A ganinsu yanar gizo, ita ce dama ta karshe da suke da ita na fafutukarsu- kama daga fafutukar neman 'yancin mata a kasashen Larabawa ko kuma a kan masu sukar lamirin gwamnati a China. A irin wadannan kasashen dai a kan yi kokarin sa ido a kan abubuwan da suke rubutawa, tamkar dai wasan buya tsakanin mage da bera ake yi tsakanin gwamnati da marubutan.

Yoani Sánchez Bloggerin in Kuba
Yoani Sánchez ta karbi lambar yabo a 2013Hoto: picture-alliance/ dpa

A shekaru 10 na tarihin gasar Bobs dai yawancin wadanda suka lashe gasar, ba a sake jin duriyarsu. Baya ga wannan, an cafke wadanda suka fara samun lambar yabon a farko-farkon fara gasar. Alal misali Yoani Sanchez 'yar kasar Cuba, wadda ta yi fice ta shafinta na fafutuka mai suna "Generation Y" wanda ke sukan yadda rayuwa ke gudana a karkashin mulkin shugaba Castro na Cuba. An dai sace wannan matar ne, inda aka yi mata dukan fitar arziki, tare da yi mata barazanar daureta dangane da irin rubuce-rubuce da take yi da ya saba wa akidun gwamnati. A shekara ta 2008 ne dai ta lashe gasar, amma sai a shekarar da ta gabata ta samu damar karbar lambar yabon na Bobs, kasancewar a baya ba ta da ikon fita daga cikin kasar ta Cuba.

Sama da rubuce-rubuce dubu uku ne aka gabatar domin shiga gasar, wadanda ya rage wa alkalan kasa da kasa na gasar 15 su bada sakamakon nazarin da suka yi domin zakulo zakarar gasar na wannan shekara, wanda aka raba shi zuwa shiyya 20, 14 daga ciki na da alaka da harshe. Sai kuma wadanda ake kira "harshen Bobs" wanda ya kunshi harshen Indonesiya da Faransanci zuwa harshen mutanen kasar Ukraine. A nan ne dai ake samun marubuta Blogs mafi inganci, wadanda ke amfani da kafofin sadarwa na zamani na wajen yayata manufofinsu na fafutuka.

Deutsche Welle Jurymitglied The Bobs 2013 Alena Popova
Alena Popova daya daga cikin alkalan BobsHoto: DW

Daya daga cikin jerin wadanda aka fitar domin shiga gasar dai shi ne wani dan fafutuka daga kasar Brazil, wanda ya rubuta takardar koke dangane da bukatar hukumomin Brazil su ba wa Edward Snowden mafakar siyasa. Sama da mutane miliyan guda suka rattaba hannu a shafin nasa dangane da wannan bukata. A karon farko dai wani marubucin Blog daga kasar Kamaru Florian Ngimbis ya shiga gasar.

Abun da ya fi daukar hankalin duniya a bana dai shi ne rikicin siyasa tsakanin Rasha da Ukraine. Dangane da haka ne ma a karo na biyu marubuciyar Blog ta kasar Rasha Alena Popova ta kasance daya daga cikin alkalan.

A watan Mayu ne dai alkalan za su gudanar da taro a birnin Berlin, inda za su gabatar da sunan wanda ya lashe gasar ta wannan shekara. Akasarin alkalan dai kwararru ne a fannonin rubutun Blogs, fafutuka, aikin jarida, masana kazalika wadanda su kansu ke da shafukan yanar gizo na Blogs.

Kuna iya kada kuri'arku a shafukan sassan #link:http://thebobs.com/english/:Ingilishi# da #link:http://thebobs.com/francais/:Faransanci#

Mawallfa: Silke Wünsch / Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Mohammad Nasiru Awal