1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kaddamar da shugaba Keita da nufin tinkarar matsalolin da ke addabar Mali

September 19, 2013

Shugaban Faransa Francoir Hollande, da kimanin shugabannin Afirka 30 ne suka halarci bukin kaddamar da sabon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita.

https://p.dw.com/p/19kqX
ARCHIV - Der Präsident Ibrahim Boubacar Keita von Mali, aufgenommen am 04.09.2013 in Bamako, Mali. Die Feierliche Zeremonie zum Amtsantritt des neuen malischen Präsidenten Ibrahim Boubacar Keita findet am 19.09.2013 in Bamako, Mali, statt. EPA/TANYA BINDRA (zu dpa-Meldung vom 19.09.2013) +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Sabon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, wanda kasarsa ta fada cikin matsanancin talauci da rigingimun siyasa da kuma tashe tashen hankula, ya yi amfani da damar da ya samu wajen bukin kaddamar dashi domin godewa al'ummomin kasa da kasa bisa gudummowar da suka bayar wajen mayar da Mali a kan turbar dimokradiyya, kimanin watanni 18 bayan kawar da zababbiyar gwamnati.

Ya yaba da irin rawar da Faransa da Kungiyar Tarayyar Afirka da ma Kungiyar Tattalin Arziki Ta Yammacin Afirka suka taka, domin kawar da 'yan tawayen da suka mamaye yankin arewacin kasar, da kuma tabbatar da cewar, kasar ta gudanar da zabe cikin 'yanci da walwala. A kan haka ne sabon shugaban na Mali, yayi alkawarin cewar, ba zai yi kasa a gwiwa ba, wajen sake daidaita lamura a kasar:

Ya ce "Zan mutunta tsarin mulkin kasar Mali da yardan Allah. Kamar yadda na yi rantsuwa a baya, zan yi namijin kokari wajen tabbatar da shugabanci gari, kuma zan kare arzikin da Allah ya horewa kasar, kuma zan dauki matakan yaki da laifukan da suka shafi cin haci da rashawa."

French President Francois Hollande speaks at the inauguration ceremony of Mali's new President Ibrahim Boubacar Keita at the Stade du 26 Mars stadium in Bamako September 19, 2013. REUTERS/Thierry Gouegnon (MALI - Tags: POLITICS)
Shugaba Francois Hollande na FaransaHoto: Reuters/Thierry Gouegnon

Muhimman kalubalen da ke gaban shugaba Keita

Sabon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, wanda dama ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 4 ga watan Satumbannan, ya ce abin da ya sa a gaba, shi ne maido da zaman lafiya, da wadata kasa da abinci, game da tallafawa kokarin maido da 'yan gudun hijirar Mali zuwa gida.

Tunda farko dai, shugaban Faransa Francoir Hollande, wanda dakarun kasarsa tare da hadin gwiwar na kasashen Afirka suka taka rawar gani wajen fatattakar 'yan tawayen na Mali, ya ce kamata yayi duniya ta ci gaba da sanya ido domin hana bata gari, sake wargaza zaman lafiyar da kasar Mali ta samu, kana ya karrama sojojin Faransa bakwai da na kasar Chadi 38 da suka mutu a lokacin yakin neman kwato yankin arewacin Mali daga hanun 'yan tawaye. Holland, ya kuma kara da cewar, a kullum, Faransa na tare da Mali:

"A yau kasar Mali ta zabarwa kanta makomarta wacce ta zabi shugabanta a zaben da aka gudanar, wanda kuma zai bude hanyar sake gina kasar, ina mai tabbatar maku cewa, kasar Faransa na tare da ku a wajen taimaka maku domin samun ci gaba da kuma sake sasanta 'yan kasar"

Mali's new President Ibrahim Boubacar Keita (standing L) arrives in his car at a stadium during his inauguration ceremony in Bamako September 19, 2013. REUTERS/Thierry Gouegnon (MALI - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Warware matsalolin Afirka, alhakin shugabanninta ne

Shugaba Hollande, ya ce gudmmowa ce kawai Faransa ta bayar, amma alhaki ne da ya rataya a wuyan shugabannin Afirka su tabbarar da tsaro a yankin.

A sakonsu na fatan alheri ga sabon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, shugaban zartarwar tarayyar Turai Herman van Rompuy da shugaban Hukumar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, sun yi alkawarin ci gaba da nuna goyon bayansu ne ga Mali a dai dai lokacin da ta bude sabon babi a tarihinta, musamman wajen shawo kan kalubalen da ke gabanta.

Dan shekaru 68 a duniya, Ibrahim Boubacar Keita, wanda ya shahara da suna IBK, tuni ya nada majalisar ministoci mai wakilai 34 , tare da kirkiro da ma'aikatar sasanta tsakanin al'umma, wadda za ta kula da bunkasa yankin arewacin Mali da kuma shawo kan matsalar kungiyoyin 'yan aware da ke yankin, kuma kasar ta tsara gudanar da zabukan majalisun dokoki a ranar 24 ga watan Nuwamba - idan Allah ya kaimu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani