1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sana'ar lemon mara sinadari

April 17, 2019

Wani matashi ya bude wurin samar da lemon kwalba wanda babu sinadari a ciki, wato, Natural Juice. A sakamakon haka ya samar da aikinyi ga matasa da dama. Jama’a dai na rububin shan wannan lemo domin karin lafiya.

https://p.dw.com/p/3GyWz
Orangensaft Orangen Glas
Hoto: Colourbox

 Kabiru Sani ya ce ya rungumi wannan sana'a domin ya riba ci zamani. Tatsar ruwan lemu ba wani sabon abu bane a biranen Najeriya, domin akwai kananan injuna da ake kira blenders da magidanta kan yi irin wannan jus din a gidaje.

Sai dai ba a cika samun jama'an da kan rungumi irin wannan a matsayin sana'a ba. Kabiru ya ce ba jus din lemu kadai suke samarwa ba. Samar da lemon kwalba wanda babu wani sinadari a cikinsa abu ne da ke samun karbuwa musamman ga jama'an da ke taka-tsamtsan a irin abincin da su ke kaiwa bakinsu.

Cinikin da jama'a irinsu ke yi wa Kabiru tuni ya ba shi damar samar wa matasa guda goma sha biyar aikin yi a wurin kasuwancinsa. Kuma bayan samar wa wadannan matasa tundun dafawa, ya ce a cikin shekaru takwas da ya kwashe yana wanann sana'a, Izuwa yanzu ya ga alfanun dogaro da kai.