1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matashi mai aikin kera gilashin makahi a Kaduna

August 14, 2019

Wani matashi a jami'ar Ahmadu Bello Zaria a Kadunan Najeriya ya kirkiro wani gilashi da idan makaho ya sa zai rinka sanar da makaho abin da ke a gabansa.

https://p.dw.com/p/3NsJw
Wannan tsohon  hoto ne da muka yi amfani da shi na wani makahon
Wannan tsohon hoto ne da muka yi amfani da shi na wani makahon Hoto: DW

Gilashin da aka sanyawa suna iglass an gabatar da shi a wajen wata gasar fasaha a Najeriya, inda ya ciwo gasar har da kyuatar kudi. Kuma ga duk wanda ya kalli wannan gilashi zai iya cewa karamar magana ce ta zama babba domin daga tattauna batun a dandali hira kamar wasa Mustapha ya ci gaba da ririta fasahar har kawo yanzu ta zama gaskiya. Sai dai saboda yadda gilashin ya hada na'urori dabam-dabam matashin ya nemi agaji daga wasu 'yan uwansa dalibai wadanda su kuma suka kara wa gilashin wasu na'urori ciki har da shigar da makaho yanar gizo.