1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kalubale kan sasantawa da 'yan Boko Haram

April 18, 2013

Ra'ayoyi sun banbanta a Tarayyar Najeriya akan sabon kwamitin da gwamnati ta dorawa alhakin ganawa da 'yayan kungiyar Boko Haram da nufin warware matsalar.

https://p.dw.com/p/18Im4
Hoto: picture alliance / dpa

Wasu daga cikin 'yayan kwamitin mai mambobi 26 na da kima a idanun jama'a. Hasali ma dai wasu daga cikinsu sun yi kokarin sassantawa da 'yayan kungiyar ta Boko haram a kashin kansu a baya. Yayin da a daya hannun kuma wasunsu suka kai ga zuwa ga takun saka da shugaban kasar da tarayyar Najeriya. Wannan Kwamitin na zaman na baya bayannan ga kokari daban daban na fuskantar rikici dake shirin shiga shekara ta hudu da kuma ya ta da hankula da asarar rayuka a daukacin kasar.

Hujjoji masu goyon baya da masu adawa da kwamitin

Duk da cewar har ya zuwa makon gobe ne za a tabbatar da rantsuwa da kama aikin 'yan kwamitin da ake sa ran za su share tsawon wasu kwanaki 60 suna aiki. sai dai tun ba akai ko ina ba kawunnan 'yan tarayyar najeriya na rabe bisa sabon matakin da ke zaman na baya baya da kuma gwamantin ke fatan zai kai ga tabbatar da zaman lafiya a daukacin arewacin kasar.

Nigeria Kano Bombenanschlag
Hare-hare da dama Boko Haram ta dauki alhaki a arewacin najeriyaHoto: Reuters

Jigo kuma daya daga cikin wadanda suka kai ga kokarin zuwa Maiduguri a baya Comrade Shehu Sani ya ce akai kasuwa ga nadin nasa da a cewar sa baya bisa hanya kuma ba zai kai ga zamowa mafitar rikicin da ke sauyin launi daga tsaro ya zuwa na siyasa yanzu haka ba. Sabon kwamitin dai na zaman kusan na tara a tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da gwamnoni na Arewa da sarakuna da ma dattawan yankin da nufin kawo karshen rikicin. Sai dai a tunanin Mallam Husaini Monguno da ke zaman masani ga harkokin tsaron kasar ta Najeriya ke nuna alamu na jan kafa da siyasa a fadar gwamnatin kasar da ke fuskantar kari matsin lambar kawo karshen rikicin a cikin lokaci.

Hanyoyin sulhu tsakanin gwamnati da Boko Haram

Babban kalubalen da ke gaban 'yan kwamitin na zaman na shawo kan 'yayan kungiyar da a baya suka ce afuwa a hannun su take, ba ga gwamantin da ta kai ga nadin 'yan kwamitin ba. Sai dai kuma jera batun diyya da ma kila nazarin musabbabin rikicin na iya shawo kai na shugabannin kungiyar da kila ba da sabon fata na sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a sashen na Arewa. Lamarin da a cewar Garba Umar Kari da ke zaman wani masani na zamantakewar al'uma a jami'ar birnin tarrayar ta Abuja, abu ne da ke iya yiwuwa in akwai sahihancin niyya.

Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya yi watsai da tayin afuwaHoto: AP

A baya dai jami'an tsaron kasar ta Nijeriya sun kai ga daya daga cikin kusoshin kungiyar a garin Kaduna a wani abun da kungiyar ta kira cin amanarta a bangaren mahukunta, ta kuma ce an sha ta ta warke. Senata Ahmed dake zaman dan majalisar dattawa daga yankin Borno ta tsakiya da ke zaman cibiyar rikicin ke bukatar taka tsantsan. Sannu a hankali dai kasar ta Najeriya ta na kan gaba a kokarin warware rikicin da ke iya tabbatar da hasahen yiwuwar rushewarta cikin wasu shekaru biyu masu zuwa.

Mawallafi: Ubale Musa Daga Abuja
Edita Mouhamadou Awal