1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: An bayyana dan takarar jam'iyyar adawa

Ramatu Garba Baba Zahradeen Umar
February 26, 2018

An soma samun rabuwar kanu a tsakanin jama'ar kasa kan batun tazarcen shugaba mai ci, Paul Biya, bayan da babbar jam'iyyar adawar kasar ta fitar da sabon dan takara da ake kallon zai iya kawo sauyi a siyasar kasar.

https://p.dw.com/p/2tMKV
NO FLASH Wahlen in Kamerun
Hoto: DW

A watan Oktoba mai zuwa ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa. Babbar jam'iyyar adawar kasar ta Kamaru ta fitar da sabon dan takara mai jini a jika. A gefe guda kuma, jam'iyya mai mulki ta Paul Biya ta nuna alamun sake tsayar da shugaba Paul Biya a matsayin dan takararta. Babban abin da ke nuna alamun buga gangar siyasa a Kamaru, shi ne tsayar da Joshua Osih da jam'iyyar adawar kasar SDF ta yi a matsayin dan takakar kujerar shugaban kasa. A tunanin jam'iyyar wannan matashin zai iya kayar da shugaba Paul Biya, wanda ke da anniyar ci gaba da shugabantar kasar, biyo bayan gyaran da gwamnatinsa ta yi a kudin tsarin mulki a shekara 2008, wanda ya ba shi damar tsayawa takara har illa ma-sha Allah.

NO FLASH Wahl in Kamerun
Shugaba Paul BiyaHoto: dapd

Alamu na nuni da cewa talakwan kasar sun fara gajiya da mulkin Biya. Da dama daga cikin jama'a na ganin ya kamata ya meka ragamar mulki ga matasa ganin tsawon shekarun da ya kwashe ya na mulki, amman masu goyon bayansa na ganin akwai bukatar barinsa ya ci gaba da mulki a sakamakon ci gaban da ya kawo musanman a fannin zaman lafiya. A yayin da jam'iyyar adawa ke tunkaho da Joshua Osih da jam'iyyar ta tsayar a matsayin dan takarar ta, magoya bayan shugaba Paul Biya suna kamfain tare da rera wakoki na jinjina ga Biya.  Armand Yedji, wani jigo ne a jam'iyya mai ci ta CPDM, kuma na hannun damar shugaba Paul Biya, ya ce sun fara shirin tunkarar babban zaben.

Shugaba Paul Biya dai ya share kusan shekaru 35 akan karagar mulki. A tsawon wadanann shekaru, John Fru Ndi, shi ne wanda ya yi  kokarin karbe mulki daga hannunsa ta hanyar zabe amman ba tare da samun nasara ba. Dan siyasan mai shekaru 77, ya ce ba zai sake tsayawa takara ba, tun da ya manyanta. Sai dai jam'iyyar shi ta SDF, ta tsayar da Joshua Osih  a matsayin wanda zai kalubalanci shugaba Paul Biya. Masu sa ido kan lamurana siyasa a Kamaru, sun zura ido don ganin ko Biya mai shekaru 86, zai nuna dattako ya janye daga takara bisa dalilai na yawan shekaru.