1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFCON: An kori Kamaru da Masar

Gazali Abdou Tasawa
July 7, 2019

A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka karo na 32 a kasar Masar kogo ne ya juye da mujiya a jiya Asabar inda aka kori mai rike da kofin wato Kamaru da kuma mai masaukin baki Masar daga cikin gasar. 

https://p.dw.com/p/3Lhem
Nigerias Stürmer Odion Ighalo feiert sein zweites Tor beim Africa Cup
Hoto: Getty Images/G. Cacace

Da farko dai Najeriya ce ta fara kafa bajintar yin waje road da Kamaru da ci uku da biyu a filin wasa na birnin Alexandria a wasan neman zuwa kwata final, kafin a cikin dare 'yan wasan kungiyar Bafana-Bafana na Afirka ta Kudu su yi wa Fira'aunonin kasar Masar 'yar ba zata da ci daya mai ban haushi a gaban 'yan kallo dubu 75 a filin wasa na birnin Alkahira. 

Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekaru 45 da Masar ta taba baras da wasa a gida a gaban 'yan kallonta a wasannin zagaye na biyu na gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka. Tuni ma dai Shugaban hukumar kwallon kafar kasar ta Masar Hani Abou Rida da ma mai horas da 'yan wasan na kasar Masar Javier Aguirre dan kasar Mexico, suka yi murabus da sauran makarrabansu baki daya. 

A ci gaba da wasanni neman tikitin zuwa kwata final a wannan Lahadi Madagaska za ta kara da Jamhuriyar Dimukuradiyyar kwango a yayin da Aljeriya za ta fafata da Guinea.