1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Kokarin magance aikata aiyyukan ta'addanci

Yusuf Bala/ASAugust 12, 2015

Mahukuntan Kamaru na cigaba da binciken kwa-kwaf a gidaje da sauran wurare don bankado wanda ke aikata aiyyukan ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1GEQm
Kamerun Mora Armee Soldaten Anti Boko Haram 07/2014
Hoto: Reinnier Kaze/AFP/Getty Images

Al'ummar Jamhuriyar Kamaru dai sun karbi wannan shiri da mahukuntan kasar suka yi na inganta tsaro a kasar tun bayan da aka tura dakarun soji da za su samar da tsaro a daukacin jami'o'in da ke kasar dan bada kariya ga dalibai, baya ga sauran wurare da su ma za su amfana da wannan tsari.

Da dama dai musamman daga bangaren daliba na ganin cewar gwamnati ta amsa kiransu na basu cikakken tsaro daidai lokacin da 'yan Boko Haram ke zafafa kai hare-hare. Bih Che Rose da ke nazarin tarihi a jami'ar ta Kamaru ta ce "a matsayinmu na manyan gobe da ake fatan za su samawa kasar makoma ta gari a nan gaba samar da tsaro a gerumu, abu ne da ke muhimmancin gaske''.

Yayin da dalibai ke farin ciki na yadda tsaro ya karu a makaratu da ma kiran kara tsaurara matakan na tsaro, a hannu guda sauran jama'a na ganin akwai bukatar fadada wannan shiri zuwa wasu wuraren kamar tashoshin mota. Paul Ndip da ke zaman guda daga cikin masu wannan tunani ya ce "ya kamata su rika lura da dukkanin ababan hawa da wadanda ke tukasu, mayakan Boko Haram kan iya daukar motar da manyan mutane ke amfani da ita idan za su kai hari".

To domin samun nasarar wannan shiri da gwamnatin Kamaru din ta bijiro da shi, ma'aikatar tsaron kasar ta nemi jama'a da su bada hadin kai wajen kaiwa ga samun nasara. Ministan tsaron kasar Edgard Alain Mebe Ngo'o ya ce "jami'an tsaro na aiki tukuru sai dai suna bukatar taimakon kowane dan kasa, kowa ya kamata ya samu ilimi kan yadda za a tunkari matsalar ta tsaro."

Wannan dai na zuwa ne bayan da jami'an sojin kasar suka bayyana sakin mutane saba'in da wani malami ke rike da su da sunan 'yan makarantar allo ko 'yan mari inda wasu daga cikinsu suka kwashe kusan shekaru hudu a hannun wannan malami wanda ake zarginsa da cusa musu akidu irin na Boko Haram.

Kamerun Soldaten gegen Boko Haram
Sojin Kamaru na sintiri a wurare da dama don tabbatar da tsaro.Hoto: Reinnier KAZE/AFP/Getty Images
Abubakar Shekau
Hare-haren Boko Haram ya sanya hukumomin Kamaru tsaurara matakan tsaro.Hoto: picture alliance/AP Photo