1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kame-kamen masu neman kafar da gwamnatin Gambiya

January 3, 2015

Jami'an tsaro a kasar Gambiya na ci gaba da cafke wadanda ake zargi da hannu wajen yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Yahya Jammeh.

https://p.dw.com/p/1EEVz
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Mahukuntan kasar Gambiya na ci gaba da cafke wadanda ake zargi da hannu wajen yunkurin kifar da gwamnatin kasar. Kawo yanzu babu tabbacin alkaluman mutanen da aka kama, sai dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun nemi jami'an tsaron su mutunta dokokin kasa da kasa.

Ranar Talata da ta gabata 'yan bindiga suka afka wa Banjul babban birnin kasar lokacin da Shugaba Yahya Jammeh yake ziyarar kasashen ketare. Jami'an diflomasiyya sun ce an hallaka hudu daga cikin maharan, yayin da saura suka tsere. Tun ranar Laraba da Shugaban kasar ta Gambiya Jammeh ya koma gida ya yi alkawarin daukan matakin ba-sani ba-sabo kan duk wanda yake da hannu wajen yunkurin kifar da gwamnatin kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal