1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamfanin Facebook ya fara tambayar Jin ra'ayin jama'a

Zulaiha Abubakar
April 3, 2018

Kamfanin Facebook ya fara turawa ma'abota ta'ammali da shi wata tambayar jin ra'ayi tare da neman shawarar yadda zai kara inganta ayyukansa.

https://p.dw.com/p/2vR2N
Facebook F8 Conference
Hoto: Getty Images/J. Sullivan

Ma'abota amfani da Facebook na cigaba da bayyana ra'ayoyin su kamar yadda Shugaban kamfanin Mark Zuckerberg ya bukata,lamarin da ya ba wasu daga cikin al'umma damar bayyana gamsuwar su ,a hannu guda kuma wasu na neman kamfanin ya yi gyara a guraren da ake tuhumar sa da sakaci.

 

A halin yanzu Facebook na fuskantar zarge-zargen da suka hada da amfani da bayanan jama'a ba tare da izinin su ba don aiwatar da ayyukan zabe a wasu kasashen da kuma rura wutar rikicin kabilanci da addini.

 

A nasa bangaren shugaban kamfanin ya bayyana burin sa na wannan shekara da kawo gagarumin gyara a Facebook.