1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kammala shirye-shiryen zabe a Najeriya

Uwais Idris/UAMarch 27, 2015

Hukumar zabe ta Najeriya ta ce ta kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da babban zaben kasar ranar Asabar, musamman batun samar da tsaro da ma kula da ma'aikatan zabe.

https://p.dw.com/p/1EyVQ
Wahlen Nigeria Ergebnis
Hoto: AP

Hukumar ta INEC ta baiyana haka ne lokacin wani taro na manema labarai tat a shirya domin fadakar da al'ummar kasa halin da ake ciki a game da gudanar da zaben mai muhimmanci ga kasar baki daya.

Taron manema labarai da shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega tare da babban daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima suka yi a Abuja, na zama dama ta karshe ta yiwa al'ummar kasar bayani, tare ma da jadadda tabbacin zaben kafin gudanar da shi a ranar Asabar.

Shugaban hukumar zabe ya bayyana cewa sun samar da cikakken tsaro a dukkanin wuraren da za'a gudanar da zabe, kuma a wasu wurare za a yi amfani da na'urar binciken jikin masu jefa kuri'a kafin a barsu su shiga. Ko ina aka kwana da batun tura sojoji a wajen zaben da ake ta takadamma a kansa? Farfesa Jega ya bayyana cewa:

‘'Duk inda ake zabe a duniyar nan yawan tanajin da ake yi ya danganta ga yanayin kalubale na yanayin tsaro, wasu kasashe saboda basu da wata matsala har a yi a gama ba zaka ga wani dan sanda a cikin wani kaya na tsaro ba, amma a wasu kasashen ko da a mazaba ka daga kai zaka ga sojoji a kan bishiya rike da bindigogi manya. Don haka ya danganci irin yadda yanayin tsaro yake , saboda haka in dai muna son a yi zabe cikin zaman lafiya to dole ne mu yi la'akari da irin yanayin da ya kamata a yi, saboda irin namu yanayin matsalar tsaro''.

Game da batun kula da lafiyar masu yiwa kasa hidima kuwa, babban darakta na hukumar, Brigadiya Janar Olawumi yace masu yiwa kasa hidima dubu 34 ne za'a yi amfani da su, wadanda dukkaninsu an yi masu inshora ta kare lafiyarsu, tare ma da samar da cibiyar da zasu iya buga waya don neman a kai masu dauki. Ya kara da cewa:

Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Hoto: DW/Gänsler

Ganin cewa ana takaddama a game da wani jami'in da ya samar da na'urarar tanatnce hannu da ake bayyana cewa yana hannun jami'an hukumar tsaro ta kasa watau SSS abinda ke jefa tsoron ko lamarin zai iya shafar zaben, Farfesa Jega ya bayyana cewa babu wata damuwa.

Za dai a gudanar da zaben ne a mazabu sama da dubu 119 a Najeriya, to sai dai hukumar ta rage yawan masu jefa kuri'a a mazabun da suka zarta kima domin kaucewa fuskantar cinkoso. Farfesa Jega yace yana fatan zasu sanar da sakamakon zaben cikin sa'oi 48 ko ma kasa da haka. Ana dai zura ido a ga yadda zaben zai gudana a Najeriyar.))