1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karancin man fetur ya janyo cece-kuce a Najeriya

Ubale MusaMarch 3, 2015

Manyan jam'iyyun kasar biyu sun koma ga siyasa da matsalar karancin man da ta mamaye kasar a halin yanzu, suna zargin juna da alhakin haddasata.

https://p.dw.com/p/1EkVz
Benzin Afrika
Hoto: picture-alliance/ dpa

Kusan daukacin gidajen man da ke da zaman kansu dai na rufe a yayin kuma da dogayen layuka suka mamaye yan kalilan din da ke samun mansu a gindin gwamnatin kasar ta Najeriya. A Abuja dai alal misali farashin na mai a kasuwannin bayan fagen da ke cin karensu babu babbaka yanzu ya ninka da sama da kaso 500 cikin 100 cikin kasa da kwanaki uku kacal a fadar Malam Usman dai wani matashi ne da na iske yana tallar man a bakin titi.

Benzin Afrika
Masu sayarwa a farashin "black market" sun yi kasuwaHoto: picture-alliance/ dpa

“ Na fita kauyen Abuja na samo, kuma ina sayarwa tsakanin naira 1,500 zuwa yanda kasuwa ta samar, kuma in mun fita muna bada cin hanci a gidajen man da kuma jami'an tsaron dake kan hanya”

Tashin farashin dalar da 'yan kasuwar kasar ke amfani da ita wajen sawo man da kusan kaso 30 cikin dari game kuma da dimbin bashin da ya kai sama da naira milliyan dubu 260 ne dai a fadar kungiyar dillallan man kasar masu zaman kansu ta IPMAN ya tilasta 'ya'yanta yanke hukuncin hakuri da tallar hajar dake zaman jini da tsoka na rayuwar al'ummar kasar ta Najeriya.

Alhaji Danladi Pasali dai na zaman sakataren kungiyar na kasa, mutumin kuma da ya ce ba riba da kuma kamar wuya 'yan kasuwar su kai ga yin tasirin da ake bukata ba tare da tsoma bakin mahukunta na Abuja wajen tabbatar da biyan basukan da suka sanya bankuna mantawa da tallafawa harkar ta saida man fetur ba yanzu

Nigeria Protest gegen Benzinpreise
Gidajen man Abuja sun rufeHoto: dapd

“Muna da ragowar basuka da ba'a biya shi ya rike, kuma wadannan kudaden, kudaden bankuna ne su kuma bankunan suna a biya wannan bashi kafin su sake bada wani aje a sayo kaya. Za mu yi taro da yammaciyar talata domin ganin yanda za'a shawo kan dillallai su sai da mai, in ba haka ba al'amura na tsaye cak”

Abun jira a gani dai na zaman mafita a tsakanin talakan dake bukatar shan mai da kuma masu siyasar da ke kallon damar daukar ra'ayi a cikin matsalar.