1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karbar cin hanci a hannun 'yan ci rani a Nijar

November 7, 2016

Wasu jandarmomi a Agadez Jamhuriyar Nijar dubunsu ta cika bayan da aka kamasu da karbar cin hanci a hannun bakin haure, abin da ke nuna irin kalubale da su ke fiskanta a hanyar zuwa Turai bayan ratsa Libiya ko Aljeriya.

https://p.dw.com/p/2SHM6
Niger Agadez Sahara Flüchtlinge Wasser
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

An Yanke wa wasu jami'an jandarmomi tara da direbobi guda biyar masu safarar daukar bakin haure zuwa Libiya hukunci, a babbar kotun Agadez. Alkalin da ya yi shari'a, bayan ya samu cikakkun hujoji sun karbi cin hanci da rashawa sai ya yanke hukunci dai dai da laifin da suka aikata. Kan wannan badakala ta safara alkali Doubou Yahaya a kotun Agadez ya bamu haske kamar haka:

"Akwai mutane da ke shigowa kasa ba tare da takardu ba wato ba bisa ka'ida ba, akwai kuma wadanda ke dafa musu sai su fitar da su daga cikin kasar ba bisa ka'ida ba, to dan haka gwamnati ta kafa doka ta hukunta duk masu irin wannan laifi da wadanda ke taimakawa a yi laifin."

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Dangance da wanan matsala ta bakin Haure akwai doka ta musamman da ke bugun duk wanda a ka kama a kan sha'anin na bakin haure kamar yadda Alkali Doubou Yahaya ke cewa:

"Duk wanda aka kama a kan irin wannan laifi na iya yi masa hukunci na daurin shekaru biyar zuwa goma a gidan kaso da tara daga miliyan daya zuwa miliyan biyar. Idan mota ce mutum ya sa ake aikin kwasar bakin ana iya kwace motar a sa cikin baitil mali na gwamnati."
 

Direbobi da ma masu fitar da bakin haure da dama ne a yanzu haka ke can gidan wakafi inda a ka yanke ma wasu shekaru biyar wasu kuma har yanzu ba su sami shari'a ba a kan haka ne ma gungun 'yan canga masu fitar da bakin hauren su ka fadi ra'ayoyin su kamar haka farawa da Bashir Ama dan caga a birnin Agadez wanda ya ce wanan doka ta Agadez ce kaweye ba ta Nijar ba.

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge
Hoto: Reuters/Akintunde Akinleye

"Akwai motoci cike da bakin haure daga sassa daban-daban na Nijar za su dauko baki su kawo Agadez su jibge ba wanda ya kama su, sai daga Agadez idan za a fita ake kamu dan haka kamata ya yi dokar ta karade fadin kasa, duk inda direba ya dauko bakin a kama shi ta haka ne za a shawo kan matsalar." 


Shi kuma Attaher Rhissa mai masukin baki ne a Agadez kira ya yi ga gwamnati ta sako 'yan uwansu dan su kula da iyalansu a sama masu wata sana'ar.

Duk da kokarin hana wannan safara ta bakin haure har yanzu daruruwan 'yan cirani ne ke rububin shigowa jihar Agadez da niyar zuwa kasar Libiya ko aljeriya a hiraraki da dama da tasha DW ta sha yi da bakin hauren, sun sha nuna cewa matsalolin yake-yake da talauci da suka addabi kasashensu ne ke sa su fitowa.