1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kare hakkin dan Adam a cikin yaki da Boko Haram

Suleiman BabayoSeptember 26, 2014

Masu rajin kare hakkin dan Adam suna nuna damuwa kan batun kare hakkin wadanda aka kama bisa zargin shiga kungiyar 'yan ta'adda, karkashin dokokin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1DLZl
Nigeria Soldaten Boko Haram ARCHIVBILD
Hoto: Reuters

Tun lokacin da dakarun Najeriya suka fara samun galaba kan yaki da 'yan kungiyar Boko Haram cikin yankin arewa maso gabashin kasar, ake samun rahotannin yadda daruruwan 'yan kungiyar ke mika wuya ga sojoji, yayin da aka kama wasu masu yawa. Amma babban abin da masu rajin kare hakkin dan Adam suke nuna damuwa shi ne kare hakkin wadanda aka kama karkashin dokokin kasar ta Najeriya.

Jami'an tsaron Najeriya na rike da tsagerun 'yan Boko Haram masu yawan gaske, sai dai yana da wuya a ce ana bin dokokin kasar da sauran dokokin duniya kan gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

A farkon wannan wata na Satumba dakarun Najeriya suka fara juya nasarar da 'yan Boko Haran ke samu a yankin arewa maso gabashin kasar, bayan hallaka 'yan kungiyar da kama wasu, lokacin fafatawa a garin Konduga na Jihar Borno.

Jerin tambayoyi ga hukumomin Najeriya

Nigeria Folteropfer Archiv 2013
Hoto: Amnesty International

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch wadda ta gudanar da bincike kan wadanda aka kama, ta ce har yanzu tambayoyin da take da su ga gwamnati su ne yadda za a raba zare da abawa, kamar yadda jami'ar kungiyar Mausi Segun ke cewa:

"Dubban mutanen da muka sani, wadanda muka tantance suke tsere a hannun hukumomin tsaro game da tashin hankalin Boko Haram na yankin arewa maso gabashin. Shin suna ina? Me yake faruwa da su? Idan an yi musu shari'a a fili ne, me ya sa mutane ba su sani ba? Irin wadannan tambayoyi muke neman gwamnati ta amsa. Mun san tsarin mulkin Najeriya ya fayyace komai, kuma ya kamata a kare doka."

Kungiyar ta ce gwamnatin kasar ta nunar da hukunta mutane 40 daga cikin wadanda aka kama bisa rikicin, amma babu karin bayani a kai, da kuma sauran da ake ci gaba da tsarewa.

Gallazawa ta fitar hankali

Ita ma kungiyar Amnesty International cikin rahoton da ta fitar a kwanakin da suka gabata, mai taken "Barka da zuwa jihannama, cin zarafi a tsarin tsaron Najeriya" ta nunar da yadda ake gallaza wa fursinoni. Rahoton ya nuna irin ukubar da wadanda aka kama ke sha a hannun jami'an tsaro. Netsanet Belay shi ne daraktan sashen kula da nahiyar Afirka a kungiyar ta Amnesty, ya yi karin haske.

"Mun ga nau'o'in cin zarafi da ake amfani da su a Najeriya. Wani abin shi ne yadda aka cire faratun mutane, da abubuwa daban-daban, da kuma saka wa mutane lantarki, sannan ana dukan mutane yayin da aka juya kansu a kasa, kafafu a sama. Ana dukan mutane na adduna, da sanduna, da kuma karafa da sauran su."

Rahotannin kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International, da sauran kungiyoyi sun nuna yadda mayakan Boko Haram da aka kama suke bacewa a gidan kurkuku.

Amnesty International - Welcome to hell fire
Zanen yadda ake gallaza wa firsinoni a NajeriyaHoto: Chijioke Ugwu Clement

Mausi Segun ta kungiyar ta Human Rights Watch ta bukaci ci gaba da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba, domin tabbatar da bin tanade-tanaden dokokin kasar da na kasashen duniya.

"Abu ne mai sauki duk wadanda suka damu da halin yadda Najeriya take daukar hakkin dan Adam, su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba, wajen mutunta dokokin kasashen duniya da na yankin, da kuma dokokin kasa."

Kungiyar Human Rights Watch ta tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti, wanda ya tantance wadanda aka kama bisa rikicin na Boko Haram, duk da cewa akwai tababa na alkaluman da kwamitin ya gano. Sai dai babban abin shi ne yadda aka kasa aiwatar da abin da kwamitin ya bukata na sakin mutane 600 da hukunta wasu daruruwa da aka yi imani sun fuskanci shari'a.