1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karim Wade zai yi shekaru 6 a gidan kaso

Pinado Abdu WabaMarch 23, 2015

Da wannan hukunci, dan tsohon shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade ba zai iya tsaywa takarar shugabancin kasar ba kamar yadda ya yi niyya.

https://p.dw.com/p/1EvaX
Senegal Karim Wade
Hoto: Reuters

Wata kotu ta musamman a Senegal ta yankewa Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar wato Abdoulaye Wade, hukuncin dauri na shekaru shidda a kurkuku, ta kuma ci shi tara na CFA billiyan dubu dari da talatin da takwas.

Wannan matakin dai, ya durkusar mi shi da duk wani fata da ya ke da shi na tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a kasar a shekara ta 2017.

Babbar jam'iyyar adawar Senegal din ce mai suna Senegalese Democratic Party wato SDP ta zabe Karim Wade a matsayin dan takarar ta, duk da cewa ya kasasnce a hannun hukumomi tun watan Afrilun shekara ta 2013.

A watan da ya gabata ne, shugaba Macky Sall wanda ya kawo karshen mulkin Abdoulaye Wade mahaifin Karim Wade na tsawon shekaru 12 ya yi gargadin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci wani yunkurin da zai kawo rudani a kasar ba.