Karin dakaru a Jamhuriya Afirka ta Tsakiya
January 1, 2013Kasashen yankin tsakiyar Afirka a wannan Talata, sun fara tura dakaru ƙasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, domin kare babban birnin ƙasar na Bangui daga faɗawa a hannun 'yan tawaye, da ke neman kawar da gwamnatin Shugaba François Bozize.
Kimanin dakaru 120 daga ƙasashen Gabon, Kongo-Brazzaville da Kamaru, sun haɗe da dakarun ƙasar Chadi 400, inda su ka ja daga, a garin Damara, wanda shi ne birnin mai mahimmaci kafin kaiwa birnin Bangui fadar gwamnati. Dakarun za su kare nausawar da 'yan tawayen da ake kira Seleka ke yi, domin hamɓarar da gwamnati.
Tun da fari shugaba Bozize ya nemi 'yan tawaye su shiga gwamnatin haɗin kan ƙasa, sannan su bar shi, ya ƙarasa wa'adinsa na mulki.
A wani labarin, an samu hargitsi a wannan Talata, a birnin na Bangui fadar gwamnati Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, inda aka zargi wani 'yan sanda da hallaka wani matashi da ake zargi da alaƙa da 'yan tawaye, kuma tashin hankalin da ya biyo baya, ya kai ga mutuwan ɗan sanda ɗaya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Yahouza Sadissou Madobi