1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin sojojin Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

March 25, 2013

Faransa ta kara yawan sojojinta da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya biyo bayan gwagwarmayar kwace madafun iko da aka yi a wannan kasa

https://p.dw.com/p/183YC
Hoto: Getty Images

Gwamnatin Faransa ta ba da sanarwar cewa tun a ranar Asabar (23.03.13) ne ta tura karin sojoji 350 zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin kare filayen saukar jiragen saman da kuma 'yan kasarta 1250 da ke zaune a can. Kenan ga baki daya sojojin Faransa kusan 600 ne ke a wannan kasa. A wannan Lahadi (24.03.13) 'yan tawayen kasar suka kwace iko da Bangui babban birnin kasar - dalilin da ya sa shugaba Francois Bozize ya arce. Su dai 'yan tawayen suna zargin Bozize ne da rashin mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka rattaba hannun akai a watan Janairu, Shugaban Faransa ,Francois Hollande ya yi kira ga 'yan tawayen da su shiga tattaunawa tare da gwamnati.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh