1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karin takunkumi kan Rasha

July 30, 2014

Kasashen Turai da Amirka sun kara kaimin takunkumi kan mahukutan kasar Rasha saboda rikicin gabashin Ukraine

https://p.dw.com/p/1Cm9D
Hoto: picture-alliance/dpa

Amirka da Tarayyar Turai sun sanar da sabbin takunkumi kan gwamnatin Rasha bisa abin da ya shafi yakin gabashin Ukraine. Shugaban kasar Amirka Barack Obama shi ne ya sanar da karin takunkumin, inda a yanzu ya hada da makamashi da makamai da kuma fannin tattalin arzikin kasar ta Rasha.

Bisa wannan takunkumin daga yanzu kungiyar EU za ta daina sayar da wasu kayayyakin fasaha ga kasar Rasha, kana za su daina yin hulda da wasu bankuna wadanda ke mallakar gwamnatin kasar.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Suleiman Babayo