1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karon battar karfe a fagen wasanni

Suleiman Babayo
September 23, 2019

A cikin shirin za a ji yadda ta kaya a gasar Bundesliga ta Jamus inda za a ji yadda ta kaya a karshen mako tsakanin kungiyoyin wasannin kwallon kafa da dama: Ku saurari shirin Labarin Wasanni.

https://p.dw.com/p/3Q5nj

A gasar Bundeliga ta nan Jamus a karshen mako bayan fafatawa tsakanin kungiyoyin kwallon kafa da dama a yanzu  kungiyar Leipzig ce ke jagorancin teburin gasar da maki 13, Bayern Munich na take mata gargada da maki 11, a yayin da Dortmund tana matsayi na uku da maki 10, a yain da a sauran filayen wasanni a nahiyar Turai ake ci gaba da kafsawa tsakanin kungiyoyin wasannin kwallon kafa, a daidai lokacin da ake ta kece reni tsakanin 'yan wasa a gasar neman cin kofin zari-ruga ta duniya da ke gudana a kasar Japan. Idan kuka saurari shirin za ku ji karin haske kan yadda Kamaru ta nada sabon mai horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta kasar.