1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar karuwar kai hari a inda ake da dandazon jama'a

Zainab Mohammed AbubakarJuly 9, 2015

Hare-hare na kara tsananta a sassa daban daban na yankin arewacin Najeriya. Rayuka masu yawa ne dai hare-haren kunar bakin wake ya yi sanadiyyarsu.

https://p.dw.com/p/1FveH
Nigeria - Bombenanschlag in Jos
Hoto: Getty Images

Najeriya na ci-gaba da fuskantar karuwar hare-haren da ake dangantawa da 'yan kungiyar Boko Haram musamman a yankin arewacin kasar. Tun dagamakon da ya shige zuwa cikin wannan makon, rayuka masu yawa ne suka salwanta daga hare-haren da aka kai a garuruwan Yobe da Jos da Zaria, da ke yankin arewacin Najeriya, daura da wadanda suka jikkata.