1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasada da rai a teku don zuwa Turai

Abdourahamane Hassane
December 5, 2016

Matasan da ke daukar kasada ta ratsa teku don zuwa Turai kan tarar da Turawa masu takardun digiri ko digiri na biyu na kame-kamen sana'a, ballantana su da basu da takardar aiki.

https://p.dw.com/p/2Tkzb
Rettungsaktion von Ärzte ohne Grenzen Mittelmeer
Hoto: DW/K. Zurutuza

Wasu matasan Afirka da ke mafarkin zuwa Turai, sun tsallake rijiya da baya a lokacin da jirgin ruwa ya kusa nutsewa da su a tekun Italiya. Abul Kasim daya daga cikin wadanda suka tsira ya baiyana irin girman hatsari da suka fuskanta.

"Idan ka baro Masar ka nufi Italiya ai kawai sai yadda Allah Ya yi da kai don mutanenmu da dama sun halaka, kuma idan kana tsakiyar ruwa batun ka yi tunanin ku koma baya ma bai taso ba don wasu za su ce a yi gaba, na yi nadama mai ya sa na dauki wannan kasada".

Italien Flüchtlinge Rettung Mittelmeer
Hoto: picture alliance/dpa/ Italian Navy Press Office

Abu Alkasim dan kasar Sudan da bai so a bayyana sunansa na asali ba, ya ce duk da irin rayukan bakin haure da ke salwanta a teku, bai cire wa wasu matasa kwadayin taka kasashen Turai ba. Amma Naziru Ibrahim Mohammed dan Afirka da ke zama a Brussels a kasar Beljiyam, na ganin matukar matasan ba su taka a sannun ba, rayuwar su za ta kare ne a yi wa kasashen Turan Hangen Dala.

"Idan ba su yi taka tsan-tsan ba, za su karar da rayuwarsu su zo nan Turai ba su tsinanawa kansu komai ba har su tsufa". Kuma idan ka zo Turai ba lallai ka yi aiki ba, kasancewar ko 'yan kasar za ka ga wani na da digiri ko ma digiri na biyu ba shi da aiki ballantana kai da ko karatun babu daga Afirka."

Abdurahim Musa Isma'il Abdullahi, dan Afirka ne da ke zama a kasar Faransa, na ganin akwai bukatar sauran matasan Afirka da su yi karatun ta nutsu a kan tunanin sadaukar da rayuwarsu don zuwa Turai.

Griechenland Migranten versuchen von Patras weiter nach Europa zu kommen
Hoto: Reuters/Y. Behrakis

Tambayar da aka yi wa Abu Alkasim da ya tsira da kyar da ga nitsewar jirgin ruwa, ko mene ne tunanin sa da komawa Afirka? Sai ya ce ba zai yiwu ba kasancewar ba shi da takardu ma'ana bai shigo ta hanyar da ta dace ba, amma da son samu ne kasarsa Sudan ta gyaru ya koma cikin 'yan uwansa da iyayensa don rayuwa mai kyau.

A yanzu dai alkaluma na nuna cewa 'yan Najeriya na kan gaba wajen yawan bakin haure da suka ratsa ta tekun Italiya don tsallakawa sauran kasashen Turai, inda alkaluman hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya a wannan shekara ke nuna cewa akalla mutane sama da 6,000 ne suka mutu a teku. Ko da yake kasar Jamus ta kaddamar da shirye-shiryen ba da tallafi ga wasu kasashen Afirka da nufin samar wa matasa aiyukan yi dan rage kwararar su zuwa Turai.