1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kudin Jamus

Zainab MohammedSeptember 18, 2008

Mahawara akan kasafin kudin shekara ta 2009 a Jamus

https://p.dw.com/p/FKor
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP

A shekaru masu gabatowa Zauren majalisar dokokin tarayyar Jamus zai zame dandalin mahawara mai karfi dangane da kasafin kuɗi na ƙasa. Sai dai ana ganin cewar wannan batu ne da zai shafi manyan jami'iyyun kasar dake gudanar da mulkin haɗaka a yanzu.

Mahawara kan wannan batu dai na kasafin kudi dai bazai kasa nasaba da matsalolin da harkokin kuɗi da kasashen duniya ke fama da ita ,daura da shirin yakin neman zaɓen shugaban gwamnati, anan tarayyar ta Jamus nan bada jimawa ba.

A mahawarar data gudana a zauren majalisar dokokin dake birnin Berlin dangane da kasafin kudi na shekara ta 2009,Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce an duk da matsalolin da kasuwannin hada-hada na kudi ke fuskanta,ana samun cigaba da faɗaɗan tattalin arziki a fadin kasar,tare da neman karin hadin kai...

"Anan ina kira ga dukkan abokan aikina dake wannan majalisa da na wannan gwamnati namu, damu mika godiya ta musamman ga ministan harkokin kudi na wannan kasa"

Merkel tace kasancewar harkokin tattalin arzikin Jamus a bayyana yake,babu yadda zata kaucewa ire-iren wadannan matsaloli baki ɗaya .Adangane da haka ne inji ta,take cigaba da mahawara da tattaunawa da shugabannin Bankunan kasar dakuma gwamnatocin sauran kasashe da matsalar ta shafa.

To sai da Shugaban jami'iyyar adawa ta FDP ,Guido Westerwelle,ya bayyana wadannan kalamai na shugabar gwamnatin akan ministan kudin,kuma dan jamiyyar SPD da kasancewar rainin hankali ne kawai..

"Wannan abun takaici ne, kasancewarsa kamar wani abune da aka rigaya aka shirya gabatarwa mutane, sai dai abun farin ciki anan shine al'ummar wannan kasa suna sane da gaskiyar lamarin,don haka inda aka faɗa musu maganar,nan zasu barta"

Merkel tace Bankunan tarayyar Jamus zasu cigaba da gudanar da harkokisu da takwarorinsu na Amurka,duk da rikicin daya ritsa da kasuwannin hada-hada na duniya musamman ita Amurka.

"Tun daga farkon hawar karagar mulkin wannan gwamnati na hadaka,ta zartar da cewar Jamus zata cigaba da bude kofofinta na kasuwanci,ta hanyar mu'amala da sauran ƙasashe ta kowane ɓangare.Kuma tana kan wannan matsayi nata ,duk da halin da ake ciki a yanzu"

Shugabar gwamnatin na Jamus tace kasafin kudin shekara ta 2009 din, nada nufin kafa tubalin rage karuwar giɓin da gwamnatin tarayya ke samu daga shekara ta 2011.Kazalika Merkel tace harkokin ilimi zai kasance abunda gwamnati zata fi mayar da fifiko akai a 'ya n shekaru masu gabatowa....

"Cigaban kowace kasa a yau,ya ta'alla ka ne akan ilimantar da al'ummanta.Kuma nayi imanin cewar ,wannan shine tushen bawa al'umma damar tofa albarkacin bakinsu"