1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kudin Nijer na 2013

December 4, 2012

Batun sayawa shugaban Nijer jirgin sama ya janyo takaddama a tsakanin mambobin majalisar dokokin kasar yayin muhawara akan kasafin kudi.

https://p.dw.com/p/16vnp
epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture alliance / dpa

A jamhuriyar Nijer majalisar dokokin kasar ta ka'da kuri'ar
amincewa da sabuwar dokar kasafin kudin kasar da kuri'a 81daga cikin 113. Sai dai 'yan majalisar dokokin na bangaren adawa guda 30 ne suka yi watsi da dokar musamman domin nuna rashin amincewarsu da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na sayarwa fadar shugaban kasa jirgin sama a cikin wasu kudade da ta samu da sunan kyauta daga kamafanin AREVA kyautar da 'yan adawar suka ce da lauje a cikin nadi.


A jimlace dai kasafin kudin kasar na Niger na shekara mai kamawa ya tashi ne fiye da CFA miliyar dubu 339 akasin miliyar 1347 a bara. A cikin Kasafin kudin sabuwar shekarar dai na CEFA inda kashi 64 daga cikin 100 na wadannan kudade za a matso su ne a cikin gida. Sai dai 'yan majalisar dokokin kawancen jam'iyyun adawa na Kasar sun yi watsi da dokar ne wacce su ka kira lissafin duna da ko a
bara gwamnatin ba ta tattara kashi 50 daga cikin 100 na kudaden da
kasafin shekarar ya yi hasashen samu.

Sai dai maganar wasu kudade miliyar 17 na CFA da gwamnatin Niger din ta ce ta samo kyauta daga hannun kamfanin AREVA na Kasar Faransa da ke aikin hakar ma'adinin URANIUM a Niger kudaden da kuma gwamnatin ta ce za ta yi amfani da miliyar 7 don sayan jirgin soja daya domin tsaron kasa sannan miliyar 10 kuma ta sayarwa fadar shugaban kasa jirgin shiga shine ya haifar da babban sabanin da ya kai ga 'yan majalisar dokoki na bangaren adawa yin watsi da dokar.

###Achtung, nicht für CMS-Flash-Galerien verwenden### FILE - In this Oct.15, 2009 file photo, an Areva Company logo is seen at the plutonium reprocessing plant Areva of Cadarache, near Aix-en-Provence, southern France. Seven people working with French nuclear reactor builder Areva were kidnapped overnight in northern Niger, a spokeswoman for the state-owned company said Thursday Sept.16, 2010. The seven were kidnapped overnight Wednesday to Thursday near the town of Arlit, Areva spokeswoman Pauline Briand said. Two of those abducted, a man and a woman, were Areva employees and French citizens and the five others worked for an Areva subcontractor, she said. (AP Photo/Claude Paris, File)
Hoto: AP

Honourable Abdulkadiri Tijjani shine jagoran rukunin 'yan majalisar dokoki na bangaren 'yan adawa, wanda ya ce basu yi na'am da bukatar ba.
Illahirin 'yan majalisar dokoki 81 na bangaren adawa ne dai suka amince da tsarin dokar wacce su ka ce abar alfahri ce musamman ganin irin yanda ta tanadi cewa kashi 64 daga cikin 100 na kudin kasar na shekara za a matso su ne a nan cikin gida sabanin shekarun baya inda sama da kashi 60 daga cikin 100 na kudin kasar na dogaransu ne daga waje.

Presidential candidate Seini Oumarou, a former prime minister under deposed president Mamadou Tandja, casts his vote in Niamey, Niger, Monday, Jan. 31, 2011. This impoverished country on the edge of the Sahara took another stab at democracy Monday when it voted for a new president and parliament that are expected to take over leadership from the military.(AP Photo/Tagaza Djibo)
Seini Oumarou, jagoran adawa a NijerHoto: AP

Da kuma ya ke mayar da martani kan batun sayan jiragen Honourable Zakari Ummaru bayyana korafin 'yan adawar yayi da cewa kyashi ne su ke dangane da abubuwan ci gaban kasar da gomnatin ta su ke nan tana yi a cikin kankanin wa'adi na kasa da shekaru biyu.


Da yammacin wannan Talatar (04. 12.12) ce majalisar dokokin Kasar ta Nijer ke gudanar da bikin rufe wanan zama na ta na nazarin kasafin kudin kasar na sabuwar shekara da ta share watanni ukku tana gudanarwa.

Mawallafi : Gazali Abdou Tasawa
Edita : Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani