1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Kasafin kudin Najeriya yayin da ake shirin zabe

December 7, 2018

Gwamnatin Najeriya da ke fuskantar zabe ta amince da kasafin da ke fuskantar rashin  tabbas bisa farashin man fetur lokacin zama na majalisar zartarwa ta kasar.

https://p.dw.com/p/39gK7
Präsident Buhari steht dem FEC vor
Hoto: Noso Isioro

Sama da Tirilyan na nairar tarrayar najeriyar guda takwas ne dai Abuja ta ce tana shirin ta kasha a cikin kasafin dake zaman na karshe ga gwamnatin   mai fuskantar zabe a badi.

A cikin makon mai zuwa ne dai ake sa ran mika daukacin kasafin ga majalisun kasar guda biyu da nufin tantancewa a cikin halin rikici a tsakanin shugabancin majalisar da ke jam'iyya ta adawa da kuma gwamnatin kasar mai mulki.

Kasafin da ke da fatan dorawa a bisa jeri na cigaban da gwamnatin ke ikirarin samu dai na zaman zakaran gwajin dafi ga gwamnatin da ke tsakanin burge 'yan kasar da sake samun zabe da kuma gazawa da kila fuskantar fushi na 'yan kasa.

Präsident Buhari und sein stellvertretender Vizepräsident Osinbajo
Hoto: Noso Isioro

To sai dai kuma bayan share tsawon awoyi kusan biyu yan majalisar zartarwar sunce basu da niyyar kara a cikin yanayi na kasar da nufin burge masu tunanin zabe a badi a fadar Hadi Sirika da ke zaman ministan harkokin sufurin sama kuma daya a cikin 'yan majalisar zartarwar.

A bara dai sai da ta kai kasar share tsawon watanni kusan bakwai tana jiran kasafin duk da kasancewar shugaban kasar da shugabannin majlaisun biyu daga jam'iyyar APC mai mulki.

Tsaka mai wuya cikin neman sauyi, ko kuma kokari na sauya da dama, in har masu gwamnatin suna shirin su fuskanci turjiya, can a  cikin  zauren majalisar dai bisa alamu kasafin na shirin samun sauki duk da tunani na siyasa a fadar Sanata Umar Kurfi da ke zaman dan majalisar dattawa daga Katsina.