1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar da tafi cin bashi a duniya

December 23, 2013

Amirka ce ke sahun farko a jerin kasashen duniya da suka fi cin bashi.

https://p.dw.com/p/1AfAP
Neue 100 Dollar Scheine Archiv 2010
Hoto: picture-alliance/dpa

Manyan kasashen duniya da suka fi karfin tattalin arziki, su ne ke sahun farko wajen cin bashi a duniya, inda Amirka ta ciri tuta. alkaluma dai na nuni da cewar, idan da za a rarraba bashin akan daukacin 'yan kasar, to, kuwa da kowane ba-Amirke zai biya yawan kudi na dalar Amirka fiye da dubu 52.

Sauran kasashen dake rufa mata baya kuwa, sun hada da Birtaniya da Faransa da Jamus da kuma Japan, domin kuwa idan mutum ya dauki kasashe 10 da suka fi cin bashi a duniya, to, kuwa wadannan kasashe biyar ne ke sama.

Don jin karin bayani, sai ku saurari shirin a kasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Mohammad Nasir Awal