1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KASAR SYRIA TA GABATAR DA SABON KUDIRI...

December 30, 2003
https://p.dw.com/p/Bvmq

Kasa da awowi 72 suka ragewa kasar Syria ta kammala wakilcin da take dashi na shekaru biyu a kwamitin sulhu na mdd,ta gabatar da wani sabon kudiri ga majalisar ta dd.

Wannan kudiri kuwa bisa rahotannin da suka iso mana,shine na bukatar ganin babu wata kasa a yankin gabas ta tsakiya dake da makami na nukiliya,don samun hakan a cewar sabon kudirin zai taimaka wajen samar da zaman lafiya tabbatacce a fadin yankin baki daya. Bugu da kari,gabatar da wannan sabon kudirin,ya samo asakline,bisa irin namijin kokarin da kasar Libya tayi na watsi da aniyarta tada na kerawa tare da mallakar makamai na nukiliya,gami kuma da maraba da sifetocin hukumar IAEA a cikin kasar. Bayan wata ganawar boye da jakadan kasar Syrien,Fayssad Mekdad yayi da wasu jamian mdd a ranar litinin din data gabata,ya fadawa yan jaridu cewa bayan gabatar da wannan sabon kudiri gaban mdd,a yanzu haka kasar ta Syria da kuma sauran takwarorinta na gabas ta tsakiya zasu zurawa sarautar Allah ido,don ganin yadda majalisar zata dauki wani mataki dangane da wannan sabon kudiri. Jakadan na Syria yaci gaba da cewa wannan sabon kudiri da kasar ta gabatar ta gabatar dashi ne a maimakon kasashe 22 na kungiyyar larabawa,kana kuma a cewar sa ya samu tabarraki na amincewa daga kasashe 117 na yan barunmu na duniya tare da kasashe 54 na cikin kungiyyar oic.

Mekdad ya kuma kara da cewa idan mdd bata amince da wannan sabon kudirin ba daga nan zuwa gobe laraba,to babu shakka kasar larabawa daya data rage a majalisar,wato Algeria zataci gaba da hobbasa na ganin kwalliya ta biya kudin sabulu dangane da wannan kudiri. Har ila yau mekdad ya kara da cewa,kasar israela har yanzu itace ta kasance kasa daya a yankin na gabas ta tsakiya dataki fitowa fili ta bayyanawa duniya cewa tana da wadan nan makamai na nukiliya ko kuma aa,to amma a kashin gaskiya a cewar Jakadan kowa ya san cewa kasar ta bani israela nada wadan nan makamai na nukiliya.

A wata ganawa da shugaban hukamar kula da makamashin nukiliya ta duniya,Mohd El baradei yayi da jaridar haareth yayi a makon daya gabata,ya tabbatar da cewa akwai alamu dake nuni da cewa kasar ta israela nada wadan nan makamai na nukiliya da kasashen na larabawa ke zargin ta dasu.

A kuwa watan Afrilun wannan shekara da muke ciki jaridar washinton Post ta Amurka ta rawaito hukumar leken asirin kasar na fadin cewa kasar ta israela nada makaman nukiliya da kuma makami mai linzami kusan 300. Kafin dai kasar ta Syria ta gabatar da wannan sabon kudiri,a baya sai da kasar masar tayi kira ga kasar ta israela data bi sahun kasar Libya na watsi da aniyarta na kerawa tare da mallakar makamin na nukiliya.

A kuwa ta bakin wani jamiin diplomasiyya na kudancin yankin na gabas ta tsakiya,fadawa kamfanin dillancin labaru na IPS yayi cewa bisa laakari da irin dangantaka ta aminci dake tsakanin kasar Amurka da israela babu shakka,wannan sabon kudiri ba zai samu cimma nasarar abin da ake zato ba,domin a cewar sa duk wata kafa ta nasar sa Amurka ka iya bi domin toshe ta.

Shi kuwa wani farfesa a jamiar masachusset ta Amurka mai suna Naseer Aruri cewa yayi babu ja kasar Amurka ba zata taba yarda ta amince da wannan sabon kudirin ba,domin kusan zata dauki wannan akudirin ne tamkar wani karan tsaye ne ake so ayi mata. Aruri yaci gaba da cewa duk da laakari da cewa wannan sabon kudiri da kasar ta Syria ta gabatar ka iya jawo rikice rikice da kuma kace nace,to babu shakka zai kuma darasi ga sauran alummar duniya na yarda da cewa i lalle kasar israela itace take kawo zaune tsaye dangane da harkokin rashin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya baki daya. Ibrahim sani