1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Afirka na bukatar hadin kai

Muntaqa AhiwaJanuary 15, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga kasashen dake fama da rikicin Boko Haram da su hada karfi da karfe wajen ganin sun dakile rikicin kungiyar.

https://p.dw.com/p/1ELM3
Boko Haram Kämpfer
Hoto: picture alliance/AP Photo

Wani manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya, Mohammed ibn Chambas, ya ce tilas ne kasashen dake fuskantar barazanr kungiyar Boko Haram su amincewa juna muddin suna son kaiga murkushe kungiyar a yankunan kasashen nasu.

Manzon na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wajibi ne kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru su hada karfi da dabaru waje guda, kafin su iya tabbatarwa kasashen duniya marsalolin su na bai daya ga yaki da kungiyar dake kokarin durkusar al'amura a kasashen nasu.

Kasa da wata guda da gudanar da babban zaben kasar Najeriya, kungiyar ta Boko Haram na karbe manyan garuruwa da sansanonin soji, tare da kashe daruruwan jama'a a shiyar arewacin kasar.

Durkusar da birnin Baga da kungiyar ta yi a hare-haren ta mafiya muni, ya sanya aka soma kiraye-kirayen agaji daga manyan kasashen duniya don dakile ta'asar da kungiyar ke yi babu kakkautawa.