1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Kasashen Afirka sun ceto kansu a MDD

January 21, 2021

Kasashen Libiya da Nijar da kuma Zimbabuwe sun gano 'yancinsu na zabe a zauren Majalisar Dinkin Duniya, bayan biyan basukan da majalisar ke bin su.

https://p.dw.com/p/3oDeU
75. UN Generalversammlung
Hoto: Iranian Presidency/Zuma/picture alliance

Mai magana da yawun Malajisar Dinkin Duniya, Farhan Haq, ya ce kasashen uku na nahiyar Afirka sun biya basukan ne bayan dakatar da su da aka yi a makon jiya, koda yake bai bayyana adadin kudaden ba.

Sai dai ta bayyana cewar kasar Libiya ta biya dala dubu bakwai da biyar da 391 yayin da Nijar ta biya dala dubu shida da 733, sai kuma kasar Zimbabuwe da ta mika dala dubu 81 da 770.

Har yanzu akwai kasashe irin su Iran da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kwango Brazaville da ma Sudan ta Kudu, wadanda duk Majalisar Dinkin Duniyar ta dakatar saboda rashin sauke nauyin da ke a kansu na rance.