1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na mika sakon ta'aziya wa Saudiya

Mahmud Yaya AzareJanuary 23, 2015

Saudiya tana ci gabatar da karbar sakwannin jimamarin rasuwar Sarki Abdallah bin Abdul Azeez da ya rasu

https://p.dw.com/p/1EPWc
Saudi-Arabiens König Abdullah ist tot
Hoto: Reuters/D. Martinez

A Saudiya ana ci gabatar da karbar sakwannin jimamarin rasuwar Sarki Abdallah bin Abdul Azeez day a rasu yayin da su kuma yan kasar ke ci gaba da kai caffa ga sabon sarkin da aka nada.

Shi dai marigayin Sarki Abdallah Bin Abdul Azeez, wanda ya rasu yana da shekaru 91, kuma da na 12 daga cikin 'ya'ya maza 36 da Sarki Abdul-Azzez bin Abdurrahman Ali Sa'ud da ya kafa masarautar ya haifa, shi ne Sarki na 6 a Masarautar, ta Ali Sa'ud, wanda kuma ake dauka a matsayin jagoran sauyin da ya kawo sauye-sauyen da suka shafi siyasa da zamantakewar 'yan kasar, da alakar kasar da ketare.

A kusan shekaru 10 da ya yi kan karagar mulki, marigayin, ya dukufa ne wajen bunkasa da raya masarautar, gami da yin rigafin duk wani abin da zai iya kawo baraka a cikin gida.

Saudi-Arabien Herrscherhaus
Hoto: picture-alliance/dpa/Kamal Mustafa

A kokarinsa na toshe duk wata kafa da baraka za ta iya bulla a masarautar, marigayin ya bullo da wani sabon tsari na kafa majalisar zabar sarki da kuma ayyana mataimakin Yarima mai jiran gado, tsarin da wasu ke ganin an farshi da kafar hagun, bayan da aka tsallake wani tsahon dan sarkin, aka nada kaninsa Yarima Migran bin Abdul Azeez da ke zama dan autan sarkin da ya kafa masarautar, a matsayin wanda zai gaji sabon sarkin da aka nada, Sarki Salman Bin Abdul Azeez, lamarin da wasu ke ganin zai iya ta da liki kadan wannan sabon sarki da aka nada mai shekaru 80 da 'yan kai ya rasu.

König Salman bin Abdul-Aziz Al Saud
Sabon Sarkin Saudiya Salman bin Abdul-Aziz Al SaudHoto: Reuters/L. Zhang

Bugu da kari, Marigayi Abdallah Bin Abdul Azeez ya shiga tarihi kan irin fadadawa da kawata masallatai biyu masu alfarma, wato Dakin Kaba da ke Makka, da kuma Masallacin Ma'aiki SAW da ke Madina, lamarin da ya saukakawa mahajjata saukin gudanar da ayyukan hajji.

Sabanin magabatansa, sarakunan na Saudiya, da suka dukufa wajen karfafar mazhabar Wahabiyanci ta 'yan Sunni a ciki da wajen kasar, Marigayin ya rage wa maluman kasar fada aji a shanin mulki, kamar yadda ya dukufa wajen yakar masu matsanancin ra'ayin Islama.

Sarakunan kasashen na Larabawa dai suma ba za su manta da marigayin ba, a kokarinsa na tare guguwar neman sauyin da ta kada a yankin wacce take barazana ga karagun mulkin sarakunan, yadda marigayin, tare da kawayensa a yankin da Kasashen Yamma, suka rikidar da boren 'yan Siriya cikin lumana ya zama na fito na fito da makamai, kamar yadda a kasashen Masar suka goyi bayan sojoji kifar da gwamnatin juyin-juya hali ta 'Yan Uwa Musulmai, yadda a Bahrain kuwa, suka tura sojojinsu don murkushe masu neman sauyi cikin lumana.

Frank-Walter Steinmeier in Saudi Arabien
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Imo