1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa za su yi zama kan Iran

Yusuf Bala Nayaya
November 12, 2017

Ana dai ci gaba da yamutsa gashin baki tsakanin kasar Saudiyya da Iran kan batutuwa da suka shafi kasashen Katar da Lebanon.

https://p.dw.com/p/2nUjT
Ägypten Kairo - Arab League Council (AL) zu Qatar und Terrorismus
Hoto: picture-alliance/Photoshot/A. Gomaa

Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana cewa za ta yi wani zaman gaggawa a ranar Lahadi ta mako mai zuwa bayan da kasar Saudiyya ta bayyana bukatar hakan. Wannan zama dai a lokacinsa za a tattauna kan abin da suka kira wuce makadi da rawa da kasar Iran ke yi musu a yankin kamar yadda ajandar taron da wani jami'in diplomasiya ya nunawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ta nunar. Kasar Bahrain da Daular Larabawa ta UAE sun nuna goyon bayansu ga bukatar ta Saudiyya kamar yadda ita ma Djibouti da ke jan ragamar kungiyar a yanzu ta nuna goyon baya. Takaddamar baya-bayan nan dai ta taso ne bayan da shugaban kasar Lebanon ya zargi Saudiyya da yin garkuwa da firaministan kasar da ya yi murabus yayin da yake wata ziyara a Saudiyyan.