1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Turai zasu ladaftar da masu halarta kudaden haramun

Kamaluddeen SaniApril 5, 2016

Alkalai a kasashen Tarayyar Jamus da Faransa da Holland gami da wasu kasashen da ke a tarayyar Turai sun dau alwashin dakile duk wasu ayyukan almundahanar halarta kudaden haramun a kasashen su.

https://p.dw.com/p/1IPU3
Panama Papers Mossack Fonseca Webseite
Hoto: picture-alliance/dpa/J.Pelaez

Wannan matakin na kasashen Turan na zuwa ne bayan wata mujallar Panama data fallasa wasu bayanai dauke da tarin sunayen mutane masu halasta kudaden haramun a duniya, a inda tayi zargin cewar futattun mutanen na gujewa biyan kudaden haraji gami da mallakar kadarorin da ba a san asalin suba a sassa daban daban na duniya.

Yanzu haka dai masu yin nazarin alamuran yau da kullun na ci gaba da diga ayar tambaya akan irin yadda futattun mutanen ke kin biyan kudaden harajin gami da kin bayyana yadda suka mallaki kadarorin su.

Kazalika sabbin wasu kungiyoyi da ke aiki da wata jibiyar binciken kwakwaf ta 'yan jaridu ta kasa da kasa da ke a Washington na cigaba da bincike akan wannan tonon asirin daya fara bayana daga wata mujallar Jamus da ke a Munich.