1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashe-kashe bayan juyin mulkin Burkina Faso

Mouhamadou Awal BalarabeSeptember 17, 2015

Sojoji sun yi harbin kan mai uwa da wabi a Ougadougou babban birnin Burkina Faso inda suka harbe wasu masu zanga-zangar kin amincewa da juyin mulki.

https://p.dw.com/p/1GYGW
Burkina Faso Ouagadougou Putsch
Hoto: Reuters/J. Penney

Akalla mutane uku sun rigamu gidan gaskiya yayin da wasu sama da 60 suka jikata a wani artabu da ya barke a Ouagadougou na Burkina Faso, tsakanin sojojin da suka yi juyin mulki da fararen hula da ke zanga-zangar kin amincewa da wannan mataki. Wadanda suka shaidar da lamarin sun bayyana wa kanfanin dillancin labaran Reuters cewar sojojin sun yi harbin kan mi uwa da wabi ne a kan masu zanga-zanga da nufin tarwatsasu bayan da aka sanar da janar Gilbert Diendere a matsayin sabon shugaban mulkin soja.

Sojojin sun rigaya sun bayyana cewar sun rusa gwamnati da kuma majalisar rikon kwarya da aka kafa bayan juyin juya hali na shekarar da ta gabata. Sannan kuma suna ci gaba da garkuwa da shugaban rikon kwarya Michel kafando da kuma firaministan na Burkina Faso Isaac Zida.

Janar Diemdere dai aboki ne na kut da kut ga shugaba Blaise Compaore wanda guguwar neman sauyi ta yi awon gaba da mulkinsa. Sai dai kuma a cikin wata hira da ya yi da tashar France 24, janar Gilbert Diendere ya bayyana cewar ya na goyon bayan sojojin kasarsa.